Auren Bogi: EFCC Ta Maka Matashi a Kotu Kan Damfarar Masoyiyarsa Ba’amurkiya $373,000
- EFCC ta kwato $13,204 daga wajen wani 'dan Najeriya da ke fuskantar shari'a kan damfara ta yanar gizo da kitsa auren bogi da wata Ba'amurkiya, da ya yi ikirarin masoyiyarsa ce
- An fara gurfanar da Nwachi Chidozie Kingsley a gaban wata kotun babbar birnin tarayya, Maitama, Abuja a watan Maris din 2023 kan aikata damfara ta yanar gizo
- Da ya gurfana a gaban kotu a ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu, wanda ake tuhumar, ya fada ma Mai shari'a Kekemeke cewa EFCC ta samu wani fili daga wajensa da motoci
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - An gurfanar da wani mutum mai suna Nwachi Chidozie Kingsley, kan zargin damfarar wata Ba'amurkiya, Nicole Kierulff Sayers kudi $373,000 kan yaudarar cewa zai aureta.
Okanne Kelechi, ya bayyana haka a ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu, 2024, yayin da yake bayar da shaida a gaban Mai shari'a U.P Kekemeke na babban kotun tarayya, Maitama, Abuja.
Yadda aka damfari Nicole Kierulff Sayers
Jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ne suka kama Kingsley a watan Mayun 2022, a wani wuri a Abuja bayan bayanan sirri ya nuna cewa yana damfara ta yanar gizo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban sashin labarai na EFCC, Dele Oyewale ya tabbatar da ci gaban a wata sanarwa da ya wallafa a shafin X na hukumar, tare da hotuna.
Hukumar ta yi karin haske kan yadda 'dan damfarar ya yaudari masoyiyarsa Ba'amurkiya sannan ya damfare ta.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa mai gabatar da kara na biyu, Okanne Kelechi, ya shaida wa mai shari’a U.P. Kekemeke cewa Shugaban sashen damfarar kudade ya samu bayanan sirri inda bayan nan aka dauki matakin.
Wasu abubuwa aka kwato daga hannun matashin?
Kelechi, jami'in EFCC, ya bayyana cewa jami'an hukumar sun samo wani fili, wani tagwayen gida a No 1, Kemme Close, off NTA Road, kusa da cocin Royal Int’l Port Harcourt, jihar Ribas, kudi $13,204, motocin Lexus Ex 350 da Toyota Venza.
Shaidan, wanda lauyan masu gabatar da kara, Fatsuma Muhammad ta jagoranta, ya bayyana cewa daga cikin hujjar da ake da su kan wanda ake tuhuma akwai"shafukan damfara daban-daban a Linkedin wadanda ya yarda cewa shi ya bude su."
Ya kuma fada ma kotu cewa martani daga ma'aikatar ayyuka da gidaje ya nuna cewa kwangilar ba na gaskiya bane,
Haka kuma wanda ake tuhumar ya yarda cewa ya aikewa Sayers da wasu 'yan kasar waje da ya damfara wasikar samun kwangila na bogi.
Mai shari’a Kekemeke ya dage sauraron karar har zuwa ranar 30 ga Afrilu, 2024 domin ci gaba da shari’ar.
An hukunta Mama Boko Haram kan zambar N40m
A wani labarin kuma, mun ji cewa kotu ta kama Aisha Alkali Wakili wacce aka fi sani da Mama Boko Haram da aikata laifi.
A ranar Litinin, 12 ga watan Fubrairu 2024, hukumar EFCC ta sanar da yin nasara a shari'ar da take yi da ita.
Asali: Legit.ng