Shugaba Tinubu da Gwamnoni Sun Fara Shirin Ɗaukar Mataki 1 da Zai Magance Matsalar Tsaro a Najeriya
- Bola Ahmed Tinubu da gwamnoni sun fara cimma matsaya kan batun kafa yan sandan jihohi da nufin kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya
- Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka ga masu ɗauko rahoto a fadar shugaban kasa ranar Alhamis
- Ya kuma bayyana sauran ayyukan da ke gaba kafin cimma kafa wannan runduna ta ƴan sandan jihohi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, tare da gwamnonin Najeriya sun amince da kafa rundunar ƴan sanda ta jihohi a kasar nan.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a na tarayya, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka yayin hira da masu ɗauko rahoton gidan gwamnati a Abuja.
Idris ya ce an cimma matsayar kafa ƴan sandan jihohin ne a taron Shugaba Tinubu da gwamnoni wanda aka yi ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Ministan, a halin yanzu za a ci gaba da tattauna yiwuwar kafa tsarin yadda ‘yan sandan jihohi zasu kasance, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Ya kuma ƙara da cewa nan gaba za a kira taruka da dama domin lalubo hanyoyon da za a bi domin kafa wannan runduna da nufin magance matsalar tsaron da ta addabi ƙasa.
Yadda za a kafa ƴan sandan jihohi
A rahoton jaridar Vanguard, Mohammed Idris ya ce:
"Amma a yanzu an fara tattaunawa kan batun kirkiro ƴan sandan jihohi, gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi sun fara tunanin kafa ƴan sandan jihohi.
"Tabbas akwai sauran taruka da za a yi nan gaba kuma akwai ayyuka masu yawa da ya kamata a yi a kan wannan batu. Amma abin da FG da gwamnatocin jihohi suka amince shi ne wajabcin samun tsari a matakin jihohi.
"Wannan na nufin anfara matsawa gaba amma kamar yadda na faɗa a baya akwai sauran ayyuka masu yawa dangane da lamarin. Za a sake zama tsakanin gwamnatoci da ƴan kasa don ganin yadda za a cimma batun."
Tinubu ya sa labule da gwamanoni
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jihohi 36 sun shiga taron gaggawa kan tsadar rayuwa da matsalar tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da IG na rundunar ƴan sanda na cikin waɗanda aka gani sun shiga wannan taro a Aso Villa
Asali: Legit.ng