Mutane Sun Shiga Fargaba Sakamakon Tashin Abun Fashewa a Legas, Bidiyo Ya Bayyana
- Mazauna Legas da masu ababen hawa sun shiga fargaba sakamakon fashewar wani abu daga wata motar dakon iskar gas
- Lamarin ya faru ne a yankin Iju Ishaga dake jihar Kudu maso Yamma da misalin ƙarfe 10:15 na daren ranar Talata, 13 ga watan Fabrairun 2024
- A halin da ake ciki, ba a iya tantance adadin waɗanda suka jikkata ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, amma masu bayar da agajin gaggawa sun isa wurin domin gudanar da aikin ceto
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Iju Ishaga, jihar Legas - Tsoro ya dabaibaye mazauna unguwar Iju Ishaga da ke Legas bayan wata babbar fashewa da ta faru a unguwar, a daren ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta tabbatar da faruwar fashewar, amma ta buƙaci mazauna yankin da kada su firgita.
A cewar NEMA, wani shago mai ɗauke da iskar gas ya fashe, wanda hakan ya haifar da wata mummunar gobara da ta shafi wasu gine-gine a titin Ogun, kusa da tashar motar Balogun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Ko’odinetan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA), Ibrahim Farinloye, ya tabbatar da faruwar lamarin kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.
Shugaban hukumar NEMA ya ce:
"Mutanen da ke kusa da Iju Ishaga su kwantar da hankalinsu, su guji firgita.
"Fashewar iskar gas da ta tashi a titin Ogun, kusa da tashar motar Balogun, jami'an hukumar kashe gobara ta jihar Legas sun samu nasarar shawo kan lamarin baki ɗaya.”
Ya ƙara da cewa:
"An rahoto cewa wani tulun iskar gas na dafa abinci da ke a wani kanti ya fashe, sannan bayan an dawo da wutar lantarki, sai gobara ta tashi."
Kalli bidiyon da jaridar Daily Trust ta sanya a nan ƙasa:
Gobarar Iju Ishaga: Hukumomi sun duƙufa aikin ceto
Hakazalika, hukumar kashe gobara ta jihar Legas ta fitar da sanarwar cewa jami'anta sun duƙufa domin ganin sun kashe gobarar.
A wata sanarwa da shugabar hukumar Margaret Adeseye ta fitar, ta bayar da tabbacin tabbatar da tsaron lafiyar jama'a.
Sai dai, har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton ba a san adadin waɗanda suka jikkata ba, ko suka rasa ransu a sakamakon fashewar.
Abun Fashewa Ya Salwantar da Ran Mutane
A wani rahoton da aka kawo a baya, kun ji cewa wani abun gashewa ya tashi a garin Galkogo dake ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Abun fashewar wanda ya tarwatse a cikin garin, ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama waɗanda lamarin ya ritsa da su.
Asali: Legit.ng