Tsadar Rayuwa: An Bukaci Shugaba Tinubu Ya Gaggauta Yin Murabus, Karin Bayani Ya Bayyana

Tsadar Rayuwa: An Bukaci Shugaba Tinubu Ya Gaggauta Yin Murabus, Karin Bayani Ya Bayyana

  • Kwamrad Toyin Raheem ya shawarci Bola Ahmed Tinubu da ya yi murabus daga matsayin shugaban kasa
  • Raheem ya bayyana halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki a yanzu da kuma garkuwa da mutane da ake yi don kudin fansa a matsayin dalilinsa na bukatar hakan
  • Legit ta rahoto cewa 'yan Najeriya na fuskantar yawancin kalubalen da jam'iyyar Shugaban kasa Tinubu, APC ta yi alkawarin magancewa shekaru tara da suka gabata

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Ikeja, jihar Lagos - Toyin Raheem, shugaban wata kungiya mai zaman kanta, wacce ke yaki da rashawa da gurbataccen shugabanci, ya bukaci Shugaban kasa Bola Tinubu da ya yi murabus.

Da yake zantawa a wata hira da Sahara TV, Raheem ya ce gwamnatin Tinubu, ta gaza duk da cewar watanninta tara kacal akan mulki.

Kara karanta wannan

Fitaccen malami ya yi hasashen sabon farashin naira kan dala, ya ce buhun shinkafa zai kai 90k

An nemi Tinubu ya yi murabus daga kujerar shugaban kasa
Tsadar Rayuwa: An Bukaci Shugaba Tinubu Ya Gaggauta Yin Murabus, Karin Bayani Ya Bayyana Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan annobar garkuwa da mutane a kasar, inda ya ce a yanzu masu garkuwa da mutane suna shiga gidaje su kai hare-hare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Raheem ya ce:

“Ba tare da fadin kalamai a kaikaice ba, kamar dai Najeriya ta gaza a matsayin kasa.
“Wannan gwamnati mai ci, ta gaza ba tare da la’akari da yawan watannin da ta yi akan mulki ba. Ba gazawa kawai ba, face mugun gazawa.
"Da haka kawai ne, mutum zai yi tsammanin ganin shugaban kasar ya yi murabus zuwa yanzu, saboda alamu sun nuna ba shi da maganin matsalar kasar nan.
"Me muke magana akai? Kamar dai ba mu da wata gwamnati a halin yanzu. Wannan ita ce gaskiyar magana.”

Jaridar Legit ta rahoto cewa tsadar rayuwa da hauhawan farashin kaya ya jefa 'yan Najeriya da dama cikin wani hali.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnan Arewa ya sharewa iyalai 70,000 hawaye, ya raba kayan abinci na miliyan 225

Tun bayan rantsar da shi a watan Mayun 2023, Shugaban kasa Tinubu yana ta aikin inganta tattalin arziki, amma manufofinsa ya gaza aiwatar da hakan.

Cire tallafin man fetur ya haifar da hauhawan farashin kaya a kasar da mutane ke rayuwa cikin talauci.

Tsadar rayuwa: Malamin addini ya gargadi Tinubu

A wani labarin, mun ji cewa yayin da ake tsaka da fama da matsin rayuwa sakamakon manufofin tattalin arziki na gwamnatin tarayya, Primate Elijah Ayodele, na cocin INRI, ya yi gagarumin gargadi ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Malamin addinin ya bayyana cewa Najeriya za ta fuskanci durkushewar tattalin arziki idan ba a dauki matakan gaggawa ba, rahoton Daily Post.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng