Yayin da Ake Zargin Take Hakkin Musulmi a Plateau, Kungiyar MURIC Ta Dauki Muhimmin Mataki
- Yayin sda ake zargin take hakkin Musulmi a Plateau, Kungiyar kare hakkin Musulmai ta MURIC ta sha alwashin daukar mataki
- Kungiyar ta ce ta yi duba ga dukkan hakkokin Musulmai da ake takewa a jihar inda ta yi alkwarin daukar muhimmin mataki kan lamarin
- Shugaban kungiyar a jihar, Sadiq Abubakar Yusuf shi ya bayyana haka yayin kaddamar da reshen kungiyar a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau – Kungiyar Kare Hakkin Musulmai (MURIC) reshen jihar Plateau ta yi alkawarin kare hakkin Musulman jihar.
Kungiyar ta ce za ta bi dukkan hanyoyin doka don tabbatar da kare hakkin nasu a jihar wanda ake zargin ana takewa.
Menene kungiyar MURIC ke cewa kan Plateau?
Tsadar rayuwa: Sanatan Kano ya yi magana kan matakan da Tinubu ke dauka, ya yi alkawari a bangarensa
Shugaban kungiyar a jihar, Sadiq Abubakar Yusuf shi ya bayyana haka yayin kaddamar da reshen kungiyar a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubakar ya ce kungiyar ta duba dukkan take hakkin Musulmai da ake yi a jihar wanda ya sabawa dokar kasa, cewar Daily Nigerian.
Wani bakon lakcara a taron, Barista Sani Abdul-Aziz ya bukaci Musulmai da kada su samu karayar zuciya lokacin da aka take musu hakki.
Matakin da MURIC ta yi alkawarin dauka
Ya kara da cewa duk lokacin da hakan ya faru za su yi dukkan mai yiwuwa don nema musu hakkinsu.
A martaninsa, Dakta Yunus Nazifi ya bukaci gwamnatin jihar da ta tabbatar da daidaito a tsakanin ‘yan jihar gaba daya.
Al'ummar Musulmai sun yi addu'ar neman nasara ga Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau.
Al’ummar Musulmi da su ka yi addu’ar sun fito daga dukkan kananan hukumomi 17 da ke jihar.
Addu’ar ta musamman an gudanar da ita ne a ranar Laraba 20 ga watan Disamba don samun nasarar gwamnan, cewar Daily Trust.
Musulmai sun yi magana kan Gwamna Caleb
A wani labarin kuma, Musulmai a jihar Plateau sun yi magana kan yadda gwamnan jihar, Caleb Mutfwang ke yi musu adalci.
Musulman sun yi addu’ar samun nasarar gwamnan inda suka bayyana Caleb a matsayin mai adalci a tsakanin al’umma.
Suka ce tabbas Gwamna Caleb ya na musu adalci a dukkan bangarorin gwamnati a jihar musamman nadin mukamai.
Asali: Legit.ng