Labari Mai Daɗi: Ƴan kasuwa Sun Rage Farashin Kayan Masarufi, Talakawa Zasu Samu Saukin Sayen Abinci
- Ƴan kasuwa a jihar Kano sun amince zasu rage farashin kayan masarufi yayin ganawa da shugaban hukumar yaƙi da rashawa, Muhyi Magaji
- Shugaban ƴan kasuwar, Ibrahim Ɗanyaro, ya ce hauhawar farashin da ake samu kamfanoni ne suke yi amma su suna nan kan tsohon farashi
- Ya kuma bai wa al'umma tabbacin cewa ba zasu ƙara farashin komai ba a kayan da ke hannunsu, zasu taimaka wajen saukakawa talakawa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Ƴan kasuwar da ke siyar da kayan masarufi waɗanda mutane ke amfani da su yau da kullum sun yanke shawarar rage farashin kayayyakin su a jihar Kano.
Shugaban ƴan kasuwa, Ibrahim Ɗanyaro ne ya bayyana haka yayin hira da ƴan jarida jim kaɗan bayan ganawa da shugaban hukumar yaƙi da rashawa ta jihar, Leadership ta rahoto.
Wane mataki aka ɗauka kan masu ɓoye kayan abinci?
Wannan ci gaban ya biyo bayan kwace wasu shaguna guda 10 da aka ɓoye kayayyaki abinci wanda hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta garƙame a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban hukumar, Muhyi Magaji ya bayyana cewa sun nemi masu rumbun ajiyar sun rasa a lokacin da suka kai samame manyan rumbunan ajiyar kayan.
Amma a cewarsa, wadanda aka bude cike suke kayayyakin abinci da suka hada da taliyar spaghetti, shinkafa, taliya, sukari, da sauran kayan abinci, rahoton The Cable.
Farashin kayan masarufi zai sauka a Kano?
Sai dai Danyaro ya ce a halin yanzu ’yan kasuwar suna sayar da kayayyakinsu a kasuwa a kan farashi kasa da farashin kamfani.
Ya ce matakin da ‘yan kasuwar suka dauka ya biyo bayan korafe-korafen da jama’a suka yi kan tashin farashin kayayyakin masarufi da tsadar rayuwa a kasar nan.
Shugaban kasuwar ya kuma sha alwashin taimaka wa hukumar wajen damke baragurbi daga cikinsu wadanda ke kara farashin kayayyaki ba bisa ka’ida ba da kuma ɓoye su.
A kalamansa, Ɗanyaro ya ce:
“Mun zo nan ne domin mu wanke kanmu daga zargin tara kayan abinci. Mun miƙa wa hukumar hujjojinmu kuma ta tabbatar da cewa ba mu da hannu a wannan lamari.
"Tashin farashin kayan masarufi da ke faruwa babu ruwan mambobin mu, kamfanoni ne suka kawo shi, kuma mun ba da shawarar daukar matakan magance halin da ake ciki.
"Mun bayyana kudurin mu na ba hukumar hadin kai wajen rage farashin kayayyaki domin jama'a su samu sauƙi, kuma zamu yi haka ne da tsohon kayan da ke hannun mu kaɗai, farashin da muke siyar da kaya bai kai na kamfani ba."
Wani jagoran kasuwa na daban, Hamisu Rabiu, ya tabbatar wa al'umma cewa zasu ci gaba da sayar da kayan da ke hannunsu a kan tsohon farashi.
Gwamnoni sun gana kan tsadar kayan abinci
A wani rahoton kuma Gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya sun fara yunƙurin lalubo hanyar tsamo mutane daga kangin tsadar rayuwa da yunwa.
A yau Litinin, 12 ga watan Fabrairu, 2024 gwamnini suka haɗu a birnin tarayya Abuja domin tattauna halin da ƙasar nan ke ciki.
Asali: Legit.ng