Gwamnan Arewa Ya Faɗi Hanyar da Mutane Za Su Bi Su Kare Kansu Daga Hare-Haren Ƴan Bindiga

Gwamnan Arewa Ya Faɗi Hanyar da Mutane Za Su Bi Su Kare Kansu Daga Hare-Haren Ƴan Bindiga

  • Gwamnan Katsina ya kara jaddada kiransa ga ɗaukacin al'umma su tashi su kare kansu daga hare-haren ta'addancin ƴan bindiga
  • Malam Dikko Umaru Radda ya ce gwamnatinsa a shirye take da taimakawa waɗanda suka shirya kare kansu da horo da kayan aiki
  • Ya kuma koka kan yadda faɗuwar darajar Naira ta haddasa hauhawar farashin kayan abinda, inda ya ce gwamnatinsa zata nemo mafita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Gwamna Malam Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya shaida wa mazauna jihar da su dauki matakan kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga.

Gwamnan ya ce maimakon mutane su riƙa dogaro da gwamnati a koda yaushe, gara su haɗa tawaga su kare kansu daga waɗannan ƴan ta'adda.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya shiga jerin waɗanda ƴan bindiga ke shirin kaiwa hari, bayanai sun fito

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda.
"Ku tashi tsaye ku kare kanku daga yan bindiga" Gwamna Radda ga Katsinawa Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda Ph.D
Asali: Facebook

Dikko Radda ya yi wannan furucin ne a ranar Juma’a a gidan gwamnati da ke Katsina yayin wani muhimmin taron gaggawa na tsaro, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron ya samu halartar sarakunan Katsina da Daura, Dakta Abdulmumini Kabir Usman da kuma Dakta Umar Farouq Umar, ƴan kasuwa da shugabannin tsaro na jihar.

Gwamna Radda ya ce:

"Dole ne mu sake duba yanayin tsaro na jihar, mu dauki matakin nemo bakin zaren warware wadannan matsalolin. Baya ga rashin tsaro, akwai wasu kalubale kamar tsadar abinci da yunwa da suka damu jama'a.
"Gwamnati ta shirya tsaf don taimakawa duk wasu mutane da suka tsara kansu a yankunansu ta hanyar ba su horo da samar musu da kayan aiki.”

Me ya kawo tsadar rayuwa a Najeriya?

Raɗɗa ya ce an samu hauhawar farashin kayayyaki ne sakamakon faduwar darajar Naira, shiyasa wasu kasashen maƙota su ke zuwa da ‘yan kudadensu ƙalilan su sayi hatsi masu yawa.

Kara karanta wannan

Hadimin gwamnan APC ya yi murabus daga mukaminsa a jihar Arewa, ya faɗi muhimmin dalili 1

“Har ila yau, akwai mutanen da ke amfani da Naira su siya kayan abinci su ɓoye da nufin tseratar da kudadensu daga yiyuwar asara sakamakon faduwar darajar kudinmu.”

Gwamnan ya ce ya zama wajibi gwamnatinsa ta tashi tsaye haiƙan ta nemo hanyar magance tsadar rayuwa gabanin abun ya fi ƙarfinta, rahoton Vanguard.

Matar Emefiele ta shiga babbar matsala

A wani rahoto na daban Hukumar EFCC ta ayyana neman matar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ruwa a jallo tare da wasu mutum uku ranar Jumu'a.

A wani hoto da ta fitar, EFCC tana zarginsu da haɗa baki da Godwin Emefiele wajen wawure maƙudan kuɗaɗe daga asusun gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262