An Bayyana Masu Hannu a Zargin Daukar Nauyin Ta'addanci da Ake Yi Wa Sanatan Arewa

An Bayyana Masu Hannu a Zargin Daukar Nauyin Ta'addanci da Ake Yi Wa Sanatan Arewa

  • Wani rahoto da ke fitowa ya bayar da ƙarin haske kan zargin ɗaukar nauyin ƴan ta’adda da ake yi wa wani Sanatan Arewa
  • Ƙungiyar Citizens Initiative for Security Awareness (CISA) ta yi watsi da zargin a ranar Juma’a, 9 ga watan Fabrairu
  • A cewar ƙungiyar, wani malamin addini da wani jami’in tsaro ne suka shirya wannan zargin da ake yi wa sanatan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar ‘Citizens Initiative for Security Awareness (CISA)’ da ke Abuja ta zargi wani limamin coci da wani jami’in tsaro mai ritaya da yaɗa labaran ƙarya game da zargin ɗaukar nauyin ta’addanci da ake yi wa wani sanata.

A yayin wani taron manema labarai a Abuja, Kabeer Salami, mataimakin kodineta (Arewa) na CISA, ya bayyana waɗannan mutane a matsayin "masu nuna ƙabilanci" da ke da nufin raba kan ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

Hedikwatar tsaro ta fadi abu 1 da za a yi don kawo karshen matsalar rashin tsaro a Najeriya

An fadi masu hannu a zargin daukar nauyin ta'addanci
Kungiyar CISA ta zargi malamin addini da wani jami'in tsaro kan zargin daukar nauyin ta'addanci kan Sanatan Arewa Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

CISA ta yi iƙirarin cewa waɗannan mutane guda biyu suna yunƙurin kawo rabuwar kai tsakanin Sanatocin Arewa da ƴan kasa ta hanyar zargin cewa wani ɗan majalisa na tallafawa ƴan bindiga da ƴan ta'adda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Guardian, Salami ya buƙaci fadar shugaban ƙasa, majalisar dattawa, jami'an tsaro, da jama'a da su yi watsi da ƙungiyoyin da ke yada labaran ƙarya, kalaman ƙiyayya, da kalaman raba kan jama'a, waɗanda za su iya haifar da tashin hankali da tsatsauran ra'ayi.

Kira domin ɗaukar mataki

CISA ta bayyana takaicin yadda mutane ke yaɗa labaran da ke neman raba kan mutane ba tare da tabbatar da sahihancinsu ba.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, ƙungiyar ta ce:

"Abin takaici ne yadda wasu ƴan Najeriya marasa kishin ƙasa, wadanda ke da alaƙa da son zuciya, sun dage kan yunƙurinsu na kawo rikici a ƙasar nan da tunzura ƴan Najeriya kan ƴan ƙasa."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sama da 100 sun kai hari a jihar Arewa, sun halaka mutane masu yawa

"Bayanai sun nuna yadda suka dage cewa Tinubu babbar barazana ne ga dimokuraɗiyyar Najeriya da haɗin kan jam'iyyar APC."

Ƙungiyar CISA ta umurci hukumomin tsaro da su kama tare da ɗaukar matakin shari’a kan duk wata ƙungiya da ke ƙoƙarin yi wa ƴan Najeriya ƙazafi da kalamai na rashin gaskiya ko dabi’un da ka iya tada rikicin ƙabilanci ko addini.

Masu Ɗaukar Nauyin Ta'addanci a Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan ma'adanai na Najeriya, Dele Alake, ya bayyana masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Najeriya.

Alake ya bayyana cewa masu yin haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba, su ne suke ɗaukar nauyin rashin tsaron da ake fama da shi a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng