Tsadar Rayuwa: Ku Yi Hakuri da Tinubu, Jigon APC Ya Roki ‘Yan Najeriya

Tsadar Rayuwa: Ku Yi Hakuri da Tinubu, Jigon APC Ya Roki ‘Yan Najeriya

  • Babban jigon jam'iyyar APC mai mulki, Dr Olamide Ohunyeye, ya magantu a kan matsi da tsadar rayuwa da al'ummar kasar ke ciki a yanzu
  • Ohunyeye ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kara hakuri da halin da ake ciki a kasar domin romon dadi na nan tafe
  • Ya bayyana cewa akwai tanadin da shugaban kasar ke yi wa kasar kuma za a fara ganin ayyukan ci gaba da more rayuwa ba da jimawa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Wani jigon jam'iyyar APC, Dr Olamide Ohunyeye, ya roki 'yan Najeriya a kan su kara hakuri da Shugaban kasa Bola Tinubu yayin da ake tsaka da fama da tsadar rayuwa a kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya fadi abu guda 1 tak da zai kawo karshen rashin tsaro a Arewa

Ohunyeye ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya bayyana a shirin "Situation Room" na wani gidan rediyo mai zaman kansa, Fresh FM a Akure, babban birnin jihar Ondo, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Jigon APC ya roki 'yan Najeriya da su kara hakuri da Tinubu
Tsadar Rayuwa: Ku Yi Hakuri da Tinubu, Jigon APC Ya Roki ‘Yan Najeriya Hoto: NESG
Asali: Twitter

Tsohon sojan mai riyata, wanda ya kasance kan gaba cikin 'yan takarar gwamnan Ondo a 2024, ya yi bayanin cewa shugaban kasar na aiki tukuru don tabbatar da ganin abubuwa sun gyaru a kasar nan da 'dan lokaci kadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Romon dadi na nan tafe, Jigon APC

Ya bayyana cewa kasar na fuskantar wani yanayi kuma za ta fito da karfi, yana mai jaddada cewa karuwar kudaden da gwamnatin tarayya ke ajiyewa a baya-bayan nan alama ce dake nuni da cewa za a sha jar miya a gaba.

Jaridar Nigerian Tribune ta nakalto jigon na APC na cewa:

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tono tushen matsalar ƴan bindiga a Arewa, ya jero hanyoyin magance su

"Yanzu da wannan (cire tallafin mai), abin da shugaban kasa ya kawowa kasar ya kai akalla naira tiriliyan shida duk shekara kuma muna san ran cewa a tsakiyar lokaci, yawancin wadannan kudade za a zuba su a harkar ci gaba a fadin kasar.
“Muna sa ran cewa tiriliyan zai taka rawa sosai wajen gina ababen more rayuwa, wajen samar da ayyukan yi, wajen rage radadin talauci ta hanyar samar da shiruye-shiryen rage radadin talauci a fadin kasar."

Ta yaya za a inganta tsaro?

Kan tsaro, jigon na APC ya ce kasar na bukatar kayayyaki da jami’an tsaro za su rika gudanar da ayyukansu a cikin kananan hukumomi daban-daban a cikin garuruwa, wadanda za su ba su damar sa ido da sanin mutane a wadannan garuruwan.

Ohunyeye ya bayyana cewa yana da tsarin ci gaba da zai farfado da tattalin arzikin kasar tare da inganta alkaluman tattalin arzikinta.

An yi zanga-zanga kan tsadar rayuwa

Kara karanta wannan

Abin Da Yasa Kano, Jigawa Ba Su Fama Da Matsalar 'Yan Bindiga: Shehu Sani Ya Magantu

A wani labarin, mun ji cewa awanni 48 bayan zanga-zangar da aka yi a Minna, babban birnin jihar Neja, sabuwar zanga-zanga ta saƙe ɓallewa a jihar da ke Arewa ta Tsakiya.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, gungun masu zanga-zanga sun mamaye tituna a garin Suleja da ke cikin jihar Neja yau Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng