Kiwon Lafiya: Gwamnan APC Ya Amince da Abu 1, Zai Ɗauki Sabbin Ma'aikata Sama da 1,000
- Gwamna Umar Bago na jihar Neja ya bada umarnin ɗaukar sabbin ma'aikatan lafiya 1,000 nan take domin cike gibi
- Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Ibrahim Dangana, ya ce gwamnan ya kuma amince a maye gurbin ma'aikatan lafiyar da suka yi ritaya
- Ya ƙara da bayanin cewa gwamnatin Bago ta kudiri aniyar inganta ɓangaren kiwon lafiya ta hanyar ɗaukar ma'aikata da samar da kayan aiki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Sakamakon ƙarancin ma'aikata a ɓangaren lafiya na jihar Neja, Gwamnati ta fara ɗaukar matakan gyara lamarin cikin gaggawa.
Gwamnatin jihar Neja karkashin jagorancin Gwamna Umar Bago ta amince da ɗaukar sabbin ma'aikatan lafiya 1,000 da kuma maye gurbin waɗanda suka yi ritaya nan take.
Kwamishinan lafiya na jiha, Dakta Ibrahim Dangana ne ya bayyana haka a Minna, babban birnin jihar Neja jiya Talata, kamar yadda Leadership ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce gwamnatin gwamna Umar Mohammed Bago na daukar matakai ne domin tabbatar da an inganta bangaren kiwon lafiya da kuma samun rahusa a fadin jihar.
Ya bayyana cewa babban kalubalen da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya a jihar shi ne na karancin ma’aikata.
Gwamnatin Bago ta ɗauki matakan gyara asibitoci
Kwamishinan ya ce za a cike giɓin da ke akwai a ɓangaren domin samar da kayan aikin kulawa da masu juna biyu, tsarin iyali da kuma gyara dangantakar asibitocin PHC a faɗin jihar.
Ya ce:
"Za a kafa tawagar da za ta sanya ido kan asibitocin matakin farko PHC da nufin gyara duk wani nau'i na ba daidai ba da ake aikatawa a ɓangaren lafiya, da kuma uwa uba cika muradan al'umma."
Kwamishinan ya nanata kudirin gwamnati na tabbatar da samar da ingantaccen kiwon lafiya mai ƙarko a jihar ta hanyar samar da isassun ma’aikata da kayan aiki da ake bukata.
Gwamnati ta maka Malami a gaban kotu
A wani rahoton na daban kuma Gwamnatin Bauchi ta shigar da sabuwar ƙara da sabbin tuhume-tuhume kan Sheikh Abdul'aziz Dutsen-Tanshi a kotun majistire.
Lauyan malamin ya bayyana cewa wanda yake karewa ya gudu ya bar gida ne bayan jami'an tsaro sun yi yunkurin damke shi.
Asali: Legit.ng