Sufetan ’Yan Sanda Ya Shiga Babbar Matsala, an Fara Farautarsa Akan Aikata Kisan Kai
- Rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta ayyana wani jami'inta mai mukamin sufeta matsayin wanda take nema ruwa a jallo
- Rundunar ta ce Sufeta Audu Omadefu ya aikata laifin kisan kai kuma ya tsere ba tare da rundunar ta san inda ya ke ba
- Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ikenga Tochukwu ta roki jama'a da su saka ido tare da kai rahoto idan sun ga jami'in
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Anambra - Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta bayyana cewa tana neman daya daga cikin jami’anta, Sufeta Audu Omadefu bisa zargin ya aikata kisan kai.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ikenga Tochukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Ya ce dan sandan mai lambar aiki AP 362178, ya tsere bayan aikata laifin da ake zarginsa da aikatawa kuma har yanzu ba a san inda yake ba, The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bukaci duk wanda yake da masaniyar inda dan sandan yake da ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda mafi kusa, yana mai cewa za a yi amfani da bayanan cikin sirri.
Abin da sanarwar ke cewa:
Sanarwar ta ce:
“Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta ayyana Sufeta Audu Omadefu matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa aikata laifin kisan kai.
“Rundunar ta bukaci duk wanda ya ga jami'in ko kuma ya samu labarin inda yake da ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda mafi kusa."
Sanarwar taci gaba da cewa:
"Ko kuma a kira lambar sashen sa ido na rundunar a lambobi kamar haka: 07039194332 ko kuma a kira PPRO akan lambar waya 08039334002.
"Duk wani bayani da aka bayar game da wannan batu za a tabbatar an yi amfani da shi cikin sirri."
Saurayi ya yi wa budurwarsa yankan rago a Bayelsa
A wani labarin kuma, rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa ta kama wani matashi mai suna Tony wanda ake zargi da kashe masoyiyarsa a tsakar dare.
Rundunar ta ce ana zargin Tony ya kashe Mis Maxuel Ebibraladei misalin karfe 3 na asubar ranar Azabar kuma ya yi yunkurin tserewa da safe lokacin da aka kama shi.
Asali: Legit.ng