Tirkashi: Wani mutum yayi kisan kai a wurin jana’izar surikarsa
- Zafin zuciya ya debi wani ya sheke dan giyar da yake bare-bare a yayin da suke tsaka da bikin binne surikarsa
- Sai dai tuni 'yan sanda sun cafke shi har sun fara gudanar da bincike don ya fuskanci hukunci
Wani mutum mai suna Julius Oliseh mai shekaru 32 da haihuwa ya kashe wani har lahira yayin bikin binne gawar surukarsa.
Wannan al'amari ya faru ne da misalin karfe 2:00pm na dare wanda ya daga hankalin duk wadanda suka halarci bikin.
Sai dai bayan shigar wanda ake tuhumar hannun jami’an tsaro ya bayyana cewa ya kashe Isikilu Shittu mai shekaru 23 ne sakamakon giya da ya bugu sannan ya soma timbele tare da neman ketawa mutuncin mutanen da suka halarci taron.
Kamar yadda ya bayyana "An shirya wannan biki ne domin girmama surukata wadda ta rasu, komai yana tafiya cikin zaman lafiya kafin daga bisani ya fara takalar mutane da rigima sakamakon shan giyar da yayi, nayi kokarin jin me yake faruwa wanda a nan ne ya afka min da fada" inji Oliseh.
KU KARANTA: Wannan rayuwa: Tsananin talauci ya sanya wata kaka ta siyar da jikarta
Wani wanda ya ganewa idonsa yadda lamarin ya auku yace mamacin an soke shi da kwalba a wuya, fuska da kuma kafadarsa, wanda da an yi hanzarin kai sa asibiti da za a iya ceto rayuwarsa.
Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar Ogun Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce "Mun samu labarin faruwar lamarin, bayan da dan uwan wanda aka kashe ya kawo kara. Sakamakon wata ‘yar hatsaniya shi kuma ya dauki kwalba ya soki dan uwansa wanda hakan yayi sandin mutuwarsa nan take".
Bayan samun labarin wannan aika-aika nan take shugaban rundunar yan sanda na ofishin yankin Mowe CSP Francis Ebhuoma, ya aike da jami'ai domin cafke wanda ya aikata laifin.
Nan take shugaban rundunar ‘yan sanda na jihar CP Ahmed Iliyasu ya bayar umarnin aikewa da shi sashen aikata manyan laifuka domin cigaba da bincike.
Daga nan ya gargadi jama'a da su guji daukar doka a hannu, domin hukumar tasu ba zata rangwantawa duk wanda aka kama da aikata laifi irin wannan ba, kanaya tabbatarwa da jama'a cewa za’a cigaba da bincike kan wanda domin yanke masa hukunci daidai da abinda ya aikata.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng