Dan sanda ya tsere bayan bindige budurwarsa a baki

Dan sanda ya tsere bayan bindige budurwarsa a baki

- Wani jami'in dan sanda a jihar Legas ya harbi budurwarsa a bakinta ya mata mugun rauni sannan ya tsere

- Faifan bidiyon budurwar da ya bazu a dandalin sada zumunta ya nuna ta cikin azaba yayin da mutane suka garzaya da ita asibiti

- Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta ce ta gano dan sandan da ya yi harbin kuma za ta kamo shi don bincike

Wani dan sanda da har yanzu ba a gano sunansa ba ya tsere bayan ya harbi budurwarsa a bakinta a Salvation Bus Stop da ke Ikeja a Legas.

An ruwaito cewa dan sanda ya gudu ya bar budurwarsa a wurin bayan aikata laifin.

DUBA WANNAN: Masu garkuwa sun sace amaryar mai gidan burodi a Katsina

Dan sanda ya tsere bayan bindige budurwarsa a baki
Kwamishinan 'Yan sandan Legas Hakeem Odumosu. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Faifan bidiyon lamarin da ke yawo a dandalin sada zumunta ya nuna matarsa tana cikin azaba yayin da wasu mutane suka taimaka suka garzaya da ita asibiti don yi mata magani.

A cikin bidiyon ana iya ganin yadda kumatun matar ya fashe saboda harsashin da ya ratsa ta bakin ta.

KU KARANTA: An cafke masu yi wa Boko Haram jigilar man fetur a Borno

An kuma nuna lokacin da matar ke zaune a kasa a asibiti tana fama da azaba yayin da ta ke jiran lititoci su zo su duba ta.

Da aka tuntube shi, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Muyiwa Adejobi ya ce, "An gano dan sandan, ba rundunar Legas ya ke ba amma an turo shi aiki a jihar Legas."

"Saurayin matar ne; za mu kamo shi. Muna tsamanin sun samu sabani ne hakan ya janyo harbin. An aike da 'yan sanda zuwa asibitin don duba matar kuma su mata tambayoyi idan ta samu sauki."

A wani labarin, wani dan gidan haya mai shekara 21 Onyemachi Mmaju, ya kashe mai gidan hayar da ya ke zama, Nonso Oyiboko a garin Ogidi a karamar hukumar Idemili na jihar Anambra.

The Punch ta ruwaito cewa an fara samun rashin jituwa tsakanin mai gidan da dan hayan ne bayan Oyiboka ya koka kan yadda Mnaju ke kawo 'yan mata gidan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164