"Ba Ku Tsira Ba": Fitaccen Malamin Addini Ya Aika Muhimmin Sako Ga Tinubu, Ya Gargadi 'Yan Siyasa

"Ba Ku Tsira Ba": Fitaccen Malamin Addini Ya Aika Muhimmin Sako Ga Tinubu, Ya Gargadi 'Yan Siyasa

  • Rabaran Ejike Mbaka, babban faston Enugu, ya bukaci Shugaban kasa Bola Tinubu da ya nuna manufar siyasa dpon rage yunwar dake kasar da kuma yakar rashin tsaro
  • Malamin addinin ya kuma yi gargadin cewa hatta ga 'yan siyasar basu tsira ba a gidajensu saboda matakin da rashin tsaro ya kai a kasar
  • Mbaka ya tuna da irin kalubalen da Tinubu ya fuskanta a hanyarsa ta zuwa fadar shugaban kasa, ya kuma yi mamakin dalilin da ya sa ya kasa yakar masu lalata tattalin arzikin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Enugu, jihar Enugu - Rabaran Ejike Mbaka, babban faston nan na jihar Enugu, ya yi kira ga Shugaban kasa Bola Tinubu da ya yaki rashin tsaro da wahalar da ake sha a kasar cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Neman tabarraki: Shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya, Ali Nuhu ya ziyarci Sarkin Kano

Malamin addinin ya yi gargadin cewa matsalar yunwar da ake fama da ita a kasar na da matukar tayar da hankali kuma dole ne a gaggauta shawo kan tabarbarewar abin.

Mbaka ya gargadi Tinubu kan rashin tsaro
"Ba Ku Tsira Ba": Fitaccen Malamin Addini Ya Aika Muhimmin Sako Ga Tinubu, Ya Gargadi 'Yan Siyasa Hoto: AMEN, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Mbaka ya tuno da kalubalen da Tinubu ya fuskanta

Da yake magana a cocinsa a ranar Lahadi, 4 ga watan Fabrairu, Mbaka ya tuna kalubale da dama da aka fuskanta a tafiyar Tinubu fadar shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewar shugaban kasar bai nuna manufar siyasa ba don magance matsalar Najeriya, Sahara Reporters ta ruwaito.

Malamin addinin ya nanata cewa yanzu aka fara yunwa a kasar nan. Ya kara da cewar hasashensa na shekaru biyu bai gama bayyana da kyau ba kuma cewa mafita ita ce kowa ya tashi tsaye kan lamarin.

Mbaka ya bayyana cewa rashin tsaro a kasar nan ya kai ga makiyaya na farmakar makiyaya manoma a gonakinsu suna daga bindigogi kirar AK47.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano zai je ya samu Tinubu su yi kus-kus kan wata gagarumar matsala 1 tak

Mbaka ya bayyana dalilin da yasa 'yan siyasa basu tsira a gidajensu ba

Malamin addinin ya ci gaba da cewa ‘yan siyasa da ke fakewa a maboyarsu ba su tsira ba saboda matakin da matsalar rashin tsaro da kasar ke fama da shi ya kai.

Ya ce:

"Hatta 'yan siyasa da suke tunanin sun tsira a gidajensu, ba ku tsira ba saboda matakin rashin tsaro zai kai bakin kofar gidajenku wata rana."

Malamin addinin ya kuma yi kira ga Shugaban kasa Tinubu da ya yaki 'yan hana ruwa gudu a ma'aikatar mai da kuma farfado da tattalin arzikin kasar.

Rabaran Mbaka ya yi hasashe kan Tinubu

A wani labarin, Rabaran Fr. Ejike Mbaka ya hango wani rikicin siyasa da zai faru a ƙasar nan wanda ya fi na Jamhuriyar Nijar, saboda ƙaruwar rashin aikin yi da a ke fama da shi a ƙasar nan.

A cikin bidiyon da aka sanya a shafin cocin na Youtube, babban faston ya yi gargaɗin cewa ubangiji yana kallon Shugaba Bola Tinubu, sannan shugaban ƙasar zai iya gyara ƙasar nan idan ya miƙa lamuransa ga ubangiji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng