Muhimmin Abu 1 da Kwankwaso Zai Ba Fifiko Idan Ya Zama Shugabn Ƙasa a 2027
- Alamu na kara nuna cewa Kwankwaso bai haƙura da neman mulkin Najeriya ba kuma zai iya sake fitowa takara a zaben 2027
- Jigon NNPP kuma ɗan takarar sanata a 2023, Farfesa Geoff Onyejegbu, ya faɗi abu 1 da tsohon gwamnan zai baiwa fifiko idan ya ƙarbi mulki
- Ya ce Kwankwaso na da gogewa da dabarun kawo ƙarshen matsalar tsaron da ake fama da ita a ƙasar nan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Babban jigon jam'iyyar NNPP, Farfesa Geoff Onyejegbu, ya bayyana cewa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, zai bada fifito kan sha'anin tsaro idan ya zama shugaban ƙasa a 2027.
Farfesa Onyejegbu, ɗan takarar sanata a zaben 2023 a inuwar NNPP kuma soja mai ritaya ya faɗi haka ne a wurin bikin murnar nasarar Kwankwasiyya a Kano.
Hakan ya biyo bayan nasarar Gwamnan Abba Kabir Yusuf a kotun ƙoli, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon ya ƙara da cewa idan Kwankwaso ya karbi madafun ikon ƙasar nan, zai dakile duk wani nau’in tada kayar baya da ta’addancin da suka addabi al’umma.
Onyejegbu ya ce a zaben da ya gabata, Kwankwaso da tawagar yakin neman zabensa sun ratsa jihohi 36 da kananan hukumomi 546 a Najeriya.
Kuma a cewarsa mutane sun yi na'am da shi har da garuruwa masu haɗari ciki hada yankunan Abuja, wanda hakan ya nuna yadda talakawa suka amince shi ne zai ceto ƙasar nan daga kangi.
Yadda Kwankwaso zai kawo ƙarshen rashin tsaro
A cewar Farfesa, tarihin Kwankwaso a matsayin tsohon gwamna da kuma ministan tsaro ya fita daban a cikin ƴan takara indai ana son magance matsalar tsaro.
Ya ce lokacin Kwankwaso na matsayin gwamnan jihar Kano, ya aiwatar da sabbin dabarun tsaro wadanda suka rage yawan laifuka da kuma dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Onyejegbu ya ce Kwankwaso ba zai tunkari matsalar tsaro da ƙarfin soji kaɗai ba, maimakon haka zai haɗa da bunƙasa zamantakewa da tattalin arziƙi da haɗa kan jama'a.
"Wannan sahihin tsari yana da matukar muhimmanci wajen magance tushen tashe-tashen hankula da ta'addanci da samar da dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kasar nan," in ji shi.
Bisa haka ya yi kira da dukkan ƴan Najeriya masu kishi da su koma bayan fitaccen ɗan siyasar na Kano domin tunkarar babban zaben 2027., rahoton Daily Nigerian.
Kotu ta hana belin mutum 5 da ake zargi da ta'addanci
A wani rahoton kuma Babbar kotun tarayya ta yi hukunci kan buƙatar belin magoya bayan Gwamna Fubara na jihar Ribas kan tuhumar ta'addanci.
Mutanen 5 da aka kama na fuskantar shari'a kan tuhume-tuhume bakwai da suka samo asali daga ƙona wani sashin majalisar dokokin Ribas.
Asali: Legit.ng