"Zaka Rasa Aikinka": Ooni Na Ife Ya Gayawa Shugaban EFCC, Ya Fadi Dalili

"Zaka Rasa Aikinka": Ooni Na Ife Ya Gayawa Shugaban EFCC, Ya Fadi Dalili

  • Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, ya bayyana cewa shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyode, ba zai daɗe a kan kujerarsa ba
  • Sarkin mai daraja ta ɗaya ya yi wannan gargadin ne ga shugaban hukumar EFCC bayan da ya yi alƙawarin bincikar fadar shugaban ƙasa, ɓangaren shari’a da majalisa
  • Sai dai Ogunwusi ya bayyana cewa mafita ga matsalolin Najeriya ita ce ta rage iko, inda ya ƙara da cewa shugaban ƙasa da gwamnoni sun fi ƙarfin a bincikesu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ooni na Ife, ya bayyana fargabar cewa shugaban EFCC, Ola Olukoyede, na iya rasa aikinsa bayan ya bayyana shirinsa.

Basaraken mai daraja ta ɗaya ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake mayar da martani kan dabarun aiki na hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ƙarƙashin jagorancin Olukoyede.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An bankado babban sanata mai daukar nauyin ta'addanci a Arewa

Shugaban EFCC ka iya rasa mukaminsa
Ooni na Ife na fargabar shugaban EFCC zai rasa mukaminsa Hoto: Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, EFCC Nigeria
Asali: Twitter

Shugaban EFCC ya bayyana shirin binciken fadar shugaban ƙasa

Olukoyede, a wani faifan bidiyo da AIT ta wallafa a shafinta na Twitter, ya ce EFCC za ta fara aikinta daga fadar shugaban ƙasa ta hanyar gudanar da bincike kan harkokin kuɗi a fadar shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce daga nan ne hukumar yaƙi da cin hanci da rashawan za ta koma majalisar tarayya, musamman hukumar majalisar tarayya.

Shugaban na EFCC ya kuma bayyana cewa binciken zai kai ga hukumar kula da harkokin shari’a ta tarayya kafin ta koma ma’aikatu domin daidaita su.

Sai dai Ooni Ogunwusi na Ife ya bayyana kalaman na Olukoyode a matsayin abin da zai iya sa ya rasa aikinsa.

Ya ƙara da cewa mutanen da yake shirin bincikar suna da ƙarfin gaske domin su ne suka ɗora shi a muƙamin kuma za su iya cire shi.

Kara karanta wannan

EFCC ta fallasa kungiyar addinin da ke taimakawa barayi karkatar da kudaden sata

Ooni na Ife yayi alƙawarin yin azumi da addu'a ga shugaban EFCC

Basaraken ya yi kira da a rage ƙarfin iko maimakon a sa shugaban ƙasa da gwamnoni su yi ƙarfi ta yadda zai yi wuya a yi bincike a kansu.

Wani ɓangare na bayanin Ooni na cewa:

"Shugaban EFCC ya faɗi wani abu a nan cewa zai binciki fadar shugaban ƙasa, ɓangaren shari’a da majalisar tarayya. Zan yi maka addu’a da azumi, wasu sun yi kafin kai, mu faɗi gaskiya."

Kalli bidiyon a nan:

EFCC Ta Ƙwato N30bn

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC ta bayyana cewa ta samu nasarar ƙwato N30bn da aka wawure a ma'aikatar jin ƙai da yaƙi da talauci.

Ana zargin dai an karkatar da kuɗaɗen ne a lokacin da tsohuwar minista Sadiya Umar Farouq, ke.jagorantar ma'aikatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel