Babban Malamin Addini Ya Fadi Wanda Ya Kamata a Ba Albashin Farko da Mutum Ya Samu
- Fasto Ituah Ighodalo na Cocin Trinity House da ke Legas ya bayyana manufar Littafi Mai Tsarki kan ƴaƴan itace na fari
- Fasto ya fassara ƴaƴan itace na fari a matsayin albashi na farko ko kudin shiga da mutum ya samu
- A cewar Ighodalo, ƴaƴan itace na fari na limamai ne ko shugabannin coci, don zama diyya saboda jajircewarsu ga aikin ubangiji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas – Ituah Ighodalo, babban limamin cocin Trinity House da ke Legas, ya bayyana cewa ƴaƴan itacen farko na shugabannin coci ne.
A wata hira da jaridar The Punch, Fasto Ighodalo ya ce ƴaƴan itace na farko shine abu na farko da mutum ya samu a lokacin girbi ko lokacin da ya fara wani sabon abu.
A cewar faston:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Sadaka ce domin nuna godiya da yabawa. Abin da littafi mai tsarki ya ce idan kun yi haka kuma kuka miƙa lamarinku ga ubangiji, sauran girbin ku ba zai lalace ba.
Ighodalo ya bayyana ma'anar ƴaƴan itace na farko a wannan zamanin
Da yake bayani kan ƴaƴan itacen farko a zamanin yau, Fasto Ighodalo ya ce albashin farko da mutum ke samu, ko kuma kuɗin shiga na farko da mutum yake samu daga kasuwanci a matsayinsa na ɗan kasuwa, shi ne ƴaƴan itacensa na farko.
A kalamansa:
"Ku zo ku gabatar da shi ga Ubangiji domin abin da za ku samu a wannan shekara ya tabbata.
"Don haka a wannan zamani, idan aka ƙara albashi daga Naira 100,000 zuwa Naira 150,000, ƙarin Naira 50,000 da za ka samu a karon farko da ka samu wannan Naira 150,000, ya zama ƴaƴan itacen farko na ƙarin da ka samu.
Ƴaƴan itacen fari na shugabannin coci ne
Da aka tambaye shi ko ƴaƴan itacen farko na limamin coci ne ko coci, Fasto Ighodalo ya ce na limaman coci ne, ya ƙara da cewa:
"Hanyar ubangiji ce ta biya su diyya saboda sadaukarwar da suka yi da kuma sadaukar da kai ga aikin Allah.
"A yanzu kuɗin suna tafiya ne ga coci, wanda hakan yake dama, daga nan coci za ta raba ga waɗanda ta ga sun dace. Wasu za su je hannun limamai, talakawa, ko wajen ginin coci da sauransu. Haka abun yake dama. Abin da ka yi shi ne ka ba ubangiji, sannan ubangiji ya ba bayinsa."
Fasto Ya Damfari Mabiyansa
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani fasto da matarsa a ƙasar Amurka ya damfari mabiyansa maƙudan kuɗi har $1.3m.
Fasto Eli Regalado ya yi wa mabiyansa ne dai shigo-shigo ba zurfi ta hanyar sayar musu da kirifto na bogi.
Asali: Legit.ng