Shugaba Tinubu Ya Aike da Saƙon Ta'aziyya Ga Mataimakin Shugaban Kasa Kan Rashin da Aka Masa

Shugaba Tinubu Ya Aike da Saƙon Ta'aziyya Ga Mataimakin Shugaban Kasa Kan Rashin da Aka Masa

  • Bola Ahmed Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar matar mahaifin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima
  • Hajja Hauwa ta rasu ne bayan fama da jinya a Maiduguri, babban birnin jihar Borno ranar Alhamis
  • Tawagar FG karkashin jagoranci NSA Nuhu Ribaɗu sun halarci jana'izar mamaciyar, inda suka yi wa Shettima ta'aziyya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya yi ta'aziyya ga mataimakinsa, Kashim Shettima bisa rasuwar abokiyar zaman mahaifiyarsa, Hajiya Hajja Hauwa Ajja Kormi.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta rahoto, matar mahaifin mataimakin shugaban ƙasa, Hajja Hauwa ta rasu ne ranar Alhamis a Maiduguri, jihar Borno.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Tinubu Ya Aike da Saƙo Ga Mataimakin Shugaban Kasa Kan Rasuwar da Aka Masa Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Marigayi Hajja Hauwa ta rasu ne bayan ta yi fama da rashin lafiya, kuma ta rasu ta bar ‘ya’ya biyar, ‘ya’yan miji da kuma jikoki da dama, Leadership ta tattaro.

Kara karanta wannan

Atiku ya bayyana ƴan takarar da yake goyon baya a zaben da za a yi ranar Asabar a jihohi 9

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi jana'izar marigayyar ne a gidanta da ke Shehuri ta Arewa kuma tawagar gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Nuhu Ribaɗu ta halarta a madadin Tinubu.

Da yake jawabi bayan sallar jana’izar, Mista Ribadu ya mika sakon ta’aziyyar Shugaba Tinubu ga Sanata Shettima tare da yi wa marigayyar addu’a.

Kakakin shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya haƙalto NSA Ribaɗu na cewa:

"Mun zo nan a madadin shugaban ƙasa domin mu yi ta'aziyya ga ɗan uwan mu kuma shugabanmu, mai girma mataimakin shugaban ƙasa kan wannan rashi da aka masa.
"Shugaban ƙasa ya yi tafiya amma ya umarci mu zo mu yi ta'aziyya a madadinsa da gwamnatin tarayya da ƴan Najeriya baki ɗaya bisa wannan rashi. Rashi ne da ya shafi kowa, muna fatan Allah ya mata rahama."

Tawagar gwamnati da ta je ta'aziyya

Tawagar da da ta je ta'aziyya garin Shettima sun haɗa da ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari, Karamin Ministan Karafa, Uba Maigari, da shugaban hukumar jin daɗin alhazai, Jalal Ahmed Arabi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Kashim Shettima ya yi babban rashi a rayuwarsa

Sauran ƴan tawagar sune, mai ba shugaban ƙasa shawara kan ayyukan bai ɗaya (ofishin mataimakin shugaban ƙasa), Aliyu Modibbo Umar, da dai sauransu.

Matawalle ya soki kalaman dattawan Katsina

A wani rahoton na daban Bello Matawalle ya caccaki dattawan jihar Katsina kan barazanar da suka yi na juya wa Tinubu baya a zaɓen 2027.

Kungiyar dattawan Katsina sun yi barazanar janye goyon bayan Arewa ga Tinubu idan bai sauya tunani kan maida rassan CBN zuwa Legas ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262