Dakarun Sojoji Sun Yi Kazamin Artabu da Ƴan Bindiga, Sun Samu Nasara a Jihar Arewa
- Sojojin Najeriya sun yi artabu yan bindiga, sun kwato mutum uku da suka sace a Jalingo, babban birnin jihar Taraba
- A wata sanarwa da rundunar Birged ta 6 ta fitar, ta ce sojojin sun tari ƴan ta'addan ne bayan tattara sahihan bayanan sirri
- Kwamandan sojojin ya bayyana cewa tuni aka sake haɗa waɗanda aka ceto da iyalansu yayin da dakaru suka sake bin masu garkuwan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Taraba - Dakarun rundunar sojin ƙasa ta Najeriya sun yi nasarar ceto wasu mutum uku da ƴan bindiga suka sace a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, dakarun sojin Bataliya ta 114 ta rundunar Birged 6 ne suka ƙwato mutanen ranar Talata, 30 ga watan Janairu da yammaci.
Wannan nasara na kunshe ne a wata sanarwa da kwamandan rundunar Birged ta 6, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya fitar kuma ta shiga hannun manema labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwan, dakarun sojojin sun kai ɗauki ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan motsin ƴan bindigan tare da mutanen da suka sace daga Ardo-Kola zuwa Yorro.
An yi musayar wuta kai zafi
Nan take bayan samun wannan bayanan, aka tura gwarazan sojoji zuwa kauyen Apawa da ke ƙaramar hukumar Yorro domin su sha kan ƴan bindigar.
Sanarwan ta ƙara da cewa sojojin sun nuna jajircewa da sanin dabarun yaƙi yayin da suka tari ƴan bindiga, suka yi artabu mai zafi.
Ƙarfin luguden wutan dakarun sojin ne ya tilasta wa ƴan bindigan arcewa domin tsira da rayuwarsu, suka bar mutane 3 da suka ɗauko a nan wurin.
Kwamandan sojojin ya ƙara da cewa tuni aka miƙa mutanen da aka ceto ga iyalan su cikin farin ciki da murna.
Bugu da ƙari, ya ce dakarun sojoji sun bi sawun masu garkuwan domin gano sansanin da suke ɓuya da kuma yiwuwar ƙara kubutar da ƙarin wasu mutane.
Yan bindiga sun kashe 15 a Benue
A wani rahoton kuma Wasu mahara ɗauke da muggan makamai sun kai sabon mummunan hari wani kauye a karamar hukumar Agatu ta jihar Benuwai.
Mazaunan garin sun bayyana cewa kawo yanzu sun gano gawarwakin mutum 15 da safiyar ranar Alhamis bayan harin.
Asali: Legit.ng