'Yan Bindiga Sun Lissafo Bukatunsu Kafin Su Sako Mutanen da Suka Sace a Abuja

'Yan Bindiga Sun Lissafo Bukatunsu Kafin Su Sako Mutanen da Suka Sace a Abuja

  • Miyagun ƴan bindigan da suka sace mutum bakwai a birnin tarayya Abuja, sun faɗi kuɗin fansan da za a ba su
  • Ƴan bindigan sun buƙaci a ba su N290m, kayan abinci da magunguna kafin su sako mutanen da suka sace
  • Sun kuma sha alwashin halaka mutum biyu daga cikin mutanen idan aka kasa biya musu buƙatunsu a kan lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wasu ƴan bindiga da suka sace mutum bakwai a yankin Kuduru na ƙaramar hukumar Bwari a Abuja, sun buƙaci a ba su N290m a matsayin kuɗin fansa.

Ƴan bindigan dai sun sace mutanen ne a ranar 28 ga watan Disamban 2023.

'Yan bindiga sun bukaci kudin fansa a Abuja
'Yan bindiga sun nemi a ba su N290m matsayin kudin fansa a Abuja Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Sauran abubuwan da ƴan bindigan suka nema kuma sun haɗa da magunguna da kayan abinci kafin su sako mutanen da suka yi garkuwa da su, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace daraktan babbar hukumar gwamnatin tarayya a kusa da sansanin soji a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen da aka sace ɗin dai sun haɗa da wata mata mai mai juna biyu, yara uku da manyan mutane huɗu, waɗanda yanzu sun shafe wata ɗaya da kwana huɗu a hannun ƴan bindigan.

Jaridar TheCable ta kawo rahoto cewa tun da farko ƴan bindigan sun buƙaci a ba su N500m, kafin su sako mutanen.

Menene buƙatun ƴan bindigan?

Wani shugaba a yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ƴan bindigan sun yi barazanar kashe mutum biyu daga cikin mutanen matukar ba a biya musu buƙatunsu kan lokaci ba.

Ya ce masu garkuwan sun kuma buƙaci kayan abinci da magunguna da barguna da rigunan sanyi.

A kalamansa:

"Sun yi mana magana mu kawo N290m domin su sako su ko kuma su kashe mutum biyu daga cikinsu. Muna da mace mai ciki da yara uku a cikinsu.

Kara karanta wannan

Bam da ƴan ta'adda suka dasa ya tashi da mutane a jihar Arewa

"Sun bukaci mu kawo buhunan shinkafa, fakitin Indomie, maganin tari, magunguna, zanin gado da rigunan sanyi don amfanin ƴan bindigan.
"Sun dage cewa dole ne sai kuɗin fansan sun cika N290m domin su sako mutanenmu."

Don haka shugaban ya roƙi Sufeto Janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun da babban hafsan sojin ƙasa, Taoreed Lagbaja, da su kawo ɗauki kan mutanen da aka sace.

Ƴan bindiga Sun Sace Darakta a Abuja

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani babban darakta a birnin tarayya Abuja.

Ƴan bindigan sun sace daraktan ne dai a kusa da wani sansanin soji da ke birnin yarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng