Mutane da Yawa Sun Mutu Yayin da Ƴan Bindiga Suka Kai Mummunan Hari Kan Bayin Allah a Arewa

Mutane da Yawa Sun Mutu Yayin da Ƴan Bindiga Suka Kai Mummunan Hari Kan Bayin Allah a Arewa

  • Wasu mahara ɗauke da muggan makamai sun kai sabon mummunan hari wani kauye a karamar hukumar Agatu ta jihar Benuwai
  • Mazaunan garin sun bayyana cewa kawo yanzu sun gano gawarwakin mutum 15 da safiyar ranar Alhamis bayan harin
  • An tattaro cewa tun makon jiya maharan suka matsa da kai hare-hare yankunan, sun tafka ta'adi mai yawa kan bayin Allah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Akalla gawarwaki 15 aka gano kawo yanzu bayan wani hari da ƴan bindiga dauke da makamai suka kai ƙauyen Ugboju da ke karamar hukumar Agatu ta jihar Benuwai.

Mazauna yankin sun bayyana cewa har yanzu akwai mutanen da suka ɓata ba a gansu ba bayan farmakin maharan ranar Laraba da yamma.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki yayin da almajiri da mai gadin makaranta suka dauki ransu a Kano

Yan bindiga sun kai sabon hari a jihar Benue.
Tsagerun Ƴan Bindigan Sun Kai Sabon Mummunan hari, Sun Halaka Bayin Allah da Yawa a Jihar Arewa Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

A cewar mutanen da ke rayuwa a kauyen, maharan sun kwashe tsawon makonni biyu kenan suna kai hare-haren ta'addanci kan bayin Allah a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani dan kauyen wanda ya zanta da wakilin jaridar Daily Trust ta wayar tarho, ya ce an gano gawarwakin mutanen da safiyar Alhamis (yau).

Ya bayyana cewa kafin ƙarshen yinin yau, ana iya gano wasu gawarwakin yayin da masu binciken ke ci gaba da tsefe dazuzzuka da nufin gano wadanda suka bata.

Yadda ƴan bindiga suka yi wa garin kawanya

Prince Inalegwu Adagole Simon, wanda ya fito daga kauyen, ya shaida wa ƴan jarida a Makurdi cewa maharan sun kewaye ƙauyen da misalin karfe 3 na yammacin Laraba.

A rahoton The Sun, Simon ya ce:

"Da misalin karfe 3 na yammacin jiya Laraba ne maharan suka shiga kauyena suka kashe mutane 15, wasu sun gudu sun bar gidajensu. Kafin yanzu, ba mu da wata matsala."

Kara karanta wannan

Miyagun 'yan bindiga sun kai ƙazamin hari, sun halaka ƴan sanda da wasu bayin Allah a jihar APC

Wane mataki aka ɗauka yanzu haka?

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Agatu a majalisar dokokin jihar, Godwin Edoh, ya yi tir da sabon harin wanda ya ce ya faru ne a ranar Laraba.

Edoh ya ce:

"Na shiga damuwa da koken jama'ar da nake wakilta, na tura hotunan gawarwakin da aka gano ga gwamna da mataimakinsa ta manhajar Whatsapp."

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai, Catherine Anene, ta ce har yanzu ba ta samu labarin faruwar lamarin ba daga DPO na Agatu ba.

Wani abu ya fashe a jihar Imo

A wani rahoton na daban Mutane da yawa sun rasa rayuwarsu a wani yankin da ake haƙo ɗanyen mai Obitti da ke ƙaramar hukumar Ohaji/Egbema a jihar Imo.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda, Henry Okoye, ya ce an samu fashewa a wurin saboda ayyuka ɓarayin man fetur a Obitti Rubber Estate.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262