Allah Ya Yi Wa Ƙanwar Tsohon Shugaban Ƙasa Rasuwa, Shugaba Tinubu Ya Aike da Saƙo Mai Muhimmanci

Allah Ya Yi Wa Ƙanwar Tsohon Shugaban Ƙasa Rasuwa, Shugaba Tinubu Ya Aike da Saƙo Mai Muhimmanci

  • Bola Ahmed Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyya bisa rasuwar Hajiya Asabe, ƙanwar tsohon shugaban ƙasa a zamanin mulkin soja, Abdulsalami Abubakar
  • Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar a Abuja, inda ya yi addu'ar Allah ya gafarta mata
  • Shugaba Tinubu ya kuma jajantawa sauran iyalan marigayyar yana mai rokon su yi koyi da kyawawan halayenta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahamed Tinubu, ya aike da saƙon ta'aziyya bisa rasuwar Hajiya Salamatu Asabe, ƙanwar tsohon shugaban kasa na soji, Janar Abdulsalami Abubakar (Mai ritaya).

Shugaba Tinubu ya yi alhinin wannan rashi ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Na hannun daman Atiku ya sake sanya labule da Tinubu a Paris, bayanai sun fito

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Aike da Sakon Ta'aziyya Ga Abdulsalami Kan Kan Rasuwar Kanwarsa Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya kuma yi ta'aziyya ga sauran dangin mamaciyar baya ga Abdulsalami bisa wannan rashi babba da suka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwan ta bayyana cewa Tinubu ya kaɗu matuƙa da samun labarin rasuwar Hajiya Asabe, tare da addu'ar Allah ya jiƙanta ya mata rahama.

Tinubu ya yi wa marigayyar ta'aziyya

Ya kuma yi addu'ar Allah ya bai wa iyalan da ta mutu ta bari damar koyi da kyawawan halayenta, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Sanarwan ta ce:

"Cikin zuciya mai rauni, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya samu labarin rasuwar Hajiya Salamatu Asabe, kanwar tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya.
"Shugaba Tinubu ya miƙa ta'aziyya ga Janar Abubakar, da iyalai, da duk wadanda suka yi alhinin wannan rashi mai raɗaɗi. Shugaban kasa ya yi addu'ar Allah ya sa iyalanta su gaji kyawawan ayyukan da ta bari.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaba Tinubu ya tona babban abu 1 da ya jefa Arewacin Najeriya cikin mawuyacin hali

"A ƙarshe ina fatan zaka karɓi ta'aziyya ta. Addu'a ta na tare da ku a daidai wannan lokaci mai wahala, Allah ya gafarta wa Hajiya Asabe ya sa ta a Aljannah."

Gwamna Zulum ya yi magana kan ci gaban Najeriya

A wani rahoton kuma Gwamna Zulum ya bayyana muhimmin abun da ya hana Najeriya ci gaba wanda a cewarsa sai kowane ɗan ƙasa ya canza kansa.

Babagana Zulum ya ce idan har ana son samun ci gaba a ƙasar na ya zama dole ƴan Najeriya su riƙa bi doka da ƙa'idoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262