Dakarun Ƴan Sanda Sun Yi Kazamin Gamurzu da Gungun Ƴan Bindiga, Sun Samu Gagarumar Nasara

Dakarun Ƴan Sanda Sun Yi Kazamin Gamurzu da Gungun Ƴan Bindiga, Sun Samu Gagarumar Nasara

  • Rundunar ƴan sanda ta samu nasarar ceto mutum 5 da aka yi garkuwa da su bayan musayar wuta da ƴan bindiga a Abuja
  • Mai magana da yawun ƴan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta bayyana yadda aka yi gurmurzu kafin samun wannan nasara
  • Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar garkuwa da mutane ta fara yawa a yankunan babban birnin ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Dakarun rundunar ƴan sandan birnin tarayya sun ceto mutum 5 daga hannun gungun ƴan garkuwa da mutane daban-daban a Abuja.

Dakarun ƴan sandan tawaga ta musamman da kuma jami'an sashin yaƙi da masu garkuwa na mutane na FCT Abuja ne suka samu wannan nasara, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: An kashe manyan ƴan bindiga 3 yayin musayar wuta a dajin iyakar Abuja da Kaduna

Sufetan yan sanda na kasa, IGP Kayode.
Yan sanda sun ceto mutum biyar da aka yi garkuwa da su a Abuja Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a ranar Litinin yayin wata hira da manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

SP Adeh ta ce:

"Ranar 27 ga watan Janairu, ƴan sandan caji ofis na Iddo suka samu kiran gaggawa cewa an ji karar harbi a yankin Sabon Lugbe, nan take aka tura dakaru wurin suka ci karo da wata mace, Blessing Eze, ɗauke da raunin harbi a kafaɗa.
"Matar ta faɗa wa jami'an tsaron cewa suna cikin tafiya ita da mijinta masu garkuwa suka tare su, suka tafi da mai gidanta. Nan take jami'an suka bazama kuma suka ceto shi a dajin Kuje."

An ceto wasu mutum 3 daga hannun masu garkuwa

Kakakin ƴan sandan ta kara da cewa a wannan rana dai wasu mutum biyu suka kai rahoto ga ƴan sanda cewa an sace abokansu uku suna tsaka da ibada a Idu Gbagyi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da yawa sun baƙunci lahira yayin da suka kai hari a jihar arewa, mutum 2 sun tsira

A cewarta, bayan samun wannan rahoton ne yan sandan ofishin Karmo karkashun jagorancin DPO suka bazama dazukan Karmo zuwa Gwagwa suka yi artabu da maharan.

A karshe dai sun samu nasarar ceto mutanen guda uku, waɗanda suka ƙunshi maza biyu da mace ɗaya, rahoton The Nation.

Sojoji sun murkushe ƴan bindiga a Kaduna

A wani rahoton kuma Rundunar sojin sama ta yi luguden wuta kan wadansu 'yan bindiga a kan babura guda 15 a jihar Kaduna.

Rundunar ta yi nasarar hallaka akalla maharan guda 30 da ke kan babura a karamar hukumar Birnin Gwari a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262