Mataimakin Shugaba Tinubu Ya Tona Babban Abu 1 Da Ya Jefa Arewacin Najeriya Cikin Mawuyacin Hali

Mataimakin Shugaba Tinubu Ya Tona Babban Abu 1 Da Ya Jefa Arewacin Najeriya Cikin Mawuyacin Hali

  • Sanata Kashim Shettima ya bayyana muhimmin abinda ya haifar da ayyukan ta'addancin ƴan bindiga a Arewacin Najeriya
  • Mataimakin shugaban kasar ya ce cin hancin da ya yi wa shugabanni katutu, shi ne tushen matsalar tsaron da ta addabi arewa
  • Ya faɗi haka ta bakin hadiminsa a wurin taron lakca da bada lambar yabo karo na 10 na gidauniyar Sir Ahmadu Bello Sardauna a Maiduguri

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce cin hanci da rashawa wanda ya yi wa harkar shugabanci katutu ne ya haifar da matsalar tsaro a arewa.

Shettima ya faɗi haka ne a wurin lakcar gidauniyar Sir Ahmadu Bello Sardauna karo na 10 wanda Gwamna Babagana Zulum ya karɓi bakunci a Maiduguri ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Shettima ya bayyana gaskiya kan shirin gwamnatin Tinubu na mayar da manyan ofisoshi zuwa Legas

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
Cin Hanci Ne Babban Abinda Ya Kawo Garkuwa da Mutane da Yan Bindiga a Arewa Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Shettima, wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin siyasa, Hakeem-Baba Ahmed, ya bayyana cin hancin jagorori a matsayin tushen rashin tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A rahoton Vanguard, ya ce:

"Bai kamata a ga shugaba yana shiga harkokin cin hanci da rashawa ba idan har yana son ya banbanta kansa da ɓarawo, ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane."

Zulum ya goyi bayan Shettima

Yayin da yake ƙara jaddada kalaman mataimakin shugaban ƙasa, Gwamna Zulum na jihar Borno ya ce matsalar cin hanci ce ta taɗiye ƙasar nan, ta hana ta ci gaba.

Ya kuma yi kira da dukkan waɗanda ke kan kujerun shugabancin al'umma da su yi kokarin kafa jagoranci na gari wanda kowa zai amfana, The Cable ta ruwaito.

Halin da ake ciki kan rashin tsaro a Najeriya

Wannan kalamai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar kiristocin kudancin Kaduna (SCKLA) ta yabawa rundunar sojojin Najeriya bisa kokarin tabbatar da tsaro.

Kara karanta wannan

An hango Tinubu yana kallon yadda aka rantsar da sabon gwamnan Kogi daga Faransa, hotuna sun bayyana

Sai dai ƙungiyar ta yi kira ga rundunar da ta ƙara zage dantse da nunka ayyukanta domin ƙara inganta tsaro mai ɗorewa a kudancin jihar Kaduna.

A nata ɓangaren, ƙungiyar kare muradan al'adun yarbawa, Afenifere, ta koka kan ƙaruwar kes din garkuwa da mutane a shiyyar Kudu maso Yamma.

Bisa haka ta buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta kiran taron masu ruwa da tsaki domin kawo ƙarshen matsalar.

Buhari Ya Jawo Za a Binciki Gwamnoni 150 da Ministoci

A wani rahoton na daban SERAP tana son sanin gaskiyar kudin da aka ba kananan hukumomi tun da aka dawo mulkin farar hula.

Daga shekarar 1999 har zuwa yanzu, kungiyar tana ikirarin an raba N40tr ga kananan hukumomi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262