Atiku Ya Yi Tsokaci Kan Ficewar Nijar, Mali da Burkina Faso Daga ECOWAS
- Atiku Abubakar ya mayar da martani kan abin da ya faru dangane da shugabancin ƙungiyar ECOWAS
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ficewar Jamhuriyar Nijar da wasu ƙasashe biyu daga ƙungiyar ECOWAS abin damuwa ne
- Sai dai Atiku ya ci gaba da cewa ƙawancen na da matuƙar tasiri ga sauran ƙasashe mambobin ƙungiyar ECOWAS ciki har da Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana matuƙar damuwarsa bayan ficewar ƙasashen Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar daga ƙungiyar ECOWAS.
Idan za a iya tunawa, shugabannin sojojin Nijar, Mali da Burkina Faso sun janye ƙasashensu daga ƙungiyar ECOWAS nan take.
Ƙasashen uku sun fitar da sanarwar haɗin gwiwa a ranar Lahadi, 28 ga watan Janairu, inda suka ce ba a ba su tabbaci kan kare tattalin arziƙinsu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Atiku ya ce kan ficewar ƙasashen 3?
Da yake mayar da martani ta hanyar wani saƙon da ya rubuta a shafinsa na X ranar Lahadi, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana ci gaban a matsayin abin damuwa kuma "al'amarin diflomasiyya mai tsanani".
Jigon na PDP ya buƙaci Najeriya da sauran ƙasashe mambobin ƙungiyar ECOWAS da su kula da harkokin tsaro.
Atiku ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:
"Rahotanni game da ficewar ƙasashe uku daga ƙungiyar ECOWAS, abun damuwa ne. Lamari ne wanda zai yi tasiri kan diflomasiyya. Dole ne mu kiyaye buƙatun ƙasan nan kan tsaron ƙasa, yaƙi da ta'addanci, ƴan bindiga, da kuma garkuwa da mutane yayin da ake ƙoƙarin shawo kan lamarin. -AA"
ECOWAS Ta Yi Martani Kan Ficewar Kasashe 3
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma ( ECOWAS) ta yi martani kan ficewar ƙasashen Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar daga cikinta.
Ƙungiyar ta yi fatali da sanarwar wacce ake yaɗa wa da ta sanar da ficewar ƙasashen uku daga cikinta, inda ta ce har yanzu ƙasashen mambobi ne a cikinta.
Asali: Legit.ng