Jama’a Sun Shiga Tashin Hankali Gobara Ta Kame Wasu Makarantun Sakandare a Anambra
- Wasu makarantu biyu a jihar Anambra sun gamu da gobara a daidai lokacin da hunturu ke ci gaba da cin kasuwa a Najeriya
- Hukumomi sun ba al’umma shawarin yadda za su ji da lamarin hunturu da kuma magance aukuwar gobara
- Ana yawan samun gobarar da ke cinye dukiyoyi a yankuna daban-daban na Najeriya, musamman a lokacin sanyi
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Jihar Anambra - Makarantun Sakandare guda biyu a Nawfia ne suka gamu da iftila’in gobara a karamar hukumar Njikoka a jihar Anambra.
Makarantun da abin ya shafa sun hada da Makarantar Sakandaren Jama’a da Makarantar Sakandaren Gwamnati, dukkansu a Nawfia.
Rahotanni sun nuna cewa gobarar da ta tashi ne da yammacin ranar Asabar daga wani daji da ke kusa da makarantun, inda ta bazu zuwa ginin makarantar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukuma ta tabbatar da faruwar lamarin
The Nation ta tattaro cewa, an samu sauki sosai, domin ba a samu asarar rai ba a barkewar gobarar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban hukumar kashe gobara na jihar, Martin Agbili ya ce mutanensa sun yifama da gobarar tare da taimakon wasu mutanen da ke wurin kafin su kai ga kashe ta.
Shawari ga al’ummar yankin
Ya bukaci shuwagabannin makarantu da dalibansu da makarantunsu ke kusa da daji da su bullo da dabarun kawar da ciyayi a nesa da harabar makarantunsu.
Hakazalika, ya ta’allaka faruwar irin wannan gobara da lokacin hunturu, kasancewar dukkan ciyayi da bishiyoyi a bushe suke.
Ya kuma shawarci al’umma da su kasance masu kulawa da kaucewa tada wuta a daji a yanayi irin wannan da ake ciki.
Gobara ta kone wani gini a Legas
A bangare guda, wani gini mai hawa 10 da ke kan titin Broad a karamar hukumar Legas Island a jihar Legas ya kama da wuta.
Daraktar hukumar kashe gobara ta jihar Legas, Margaret Adeseye ce ta bayyana hakan ga jaridar Punch a ranar Lahadi.
Gobarar da har yanzu ba a tantance musabbabin tashinta ba ta rutsa da shahararren ginin Mandilas da ke yankin tun daga hawa na farko na ginin har ta zarce zuwa hawa na hudu.
Asali: Legit.ng