“Wallahi Duk Wadanda Suka Yaudari Mutane da Musulmi da Musulmi Sai Sun Hadu da Allah”, Mahdi Shehu
- Fitaccen mai fafutuka, Mahdi Shehu ya caccaki gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu da Kashim Shettima kan halin da yan kasar ke ciki
- Mahdi ya kuma bayyana cewa duk wadanda suka yaudari mutane suka tallata masu Tinubu da Shettima da sunan tikitin Musulmi da Musulmi za su je su tarar da Allah
- Dan kasuwar yana martani ne akan bidiyon wata tsohuwa da tace ta yi kuka da hawaye saboda rashin abinci da yunwa
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Abuja - Dan kasuwar Najeriya kuma mai fafutuka, Mahdi Shehu, ya caccaki gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu saboda mawuyacin halin da mutane ke ciki a kasar.
A wata wallafa da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya), Mahdi ya kuma caccaki wadanda suka tallata Tinubu da Kashim karkashin tikitin Musulmi da Musulmi.
An yaudari mutane da Muslim-Muslim, Mahdi Shehu
Ya ce lallai sai Allah ya kama duk wadanda suka yaudari al'umma har suka zabi gwamnatin APC mai ci da sunan Musulunci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malaman addinin musulunci da-dama sun tallata tikitin Bola Tinubu/Kashim Shettima a yau kuma wasunsu suna kuka da gwamnati.
Mahdi ya yi martani ne a kan bidiyon wata tsohuwar mata da ta koka tare da zubar da hawaye saboda tsananin yunwa.
Yadda tsohuwa ta yi kuka saboda yunwa
A cikin bidiyon da ya daura a shafin nasa, an gano lokacin da wasu mata suka tsaya a mota suna rabawa bayin Allah abinci.
Ko da suka bai wa wata tsohuwa nata kason a cikin wata yar leda, sai matar ta fashe da kuka tare da yi masu addu'a.
An jiyo matar tana cewa:
"Har kuka na yi wa yunwa, lada kun gamu da shi girman Allah. Yanzu na yi kuka na gaji kan yunwa"
Mahdi ya rubuta a shafin nasa:
"Wallahi duk wadanda suka yaudari mutane suka saida Tinubu da kashim a karkashin yaudarar Muslim- Muslim sai sun hadu da Allah.
"Ka ya nan sun saka mutane a cikin halin bala'i yumwa, taluci, fatara da.kuncin rayuwa, a lokacin da ake wadaka da satar sukiyar kasa. Allah ya isar mana."
Ga wallafar a kasa:
Shettima ya magantu kan mayar manyan ofisoshi Legas
A wani labarin kuma, mun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya ƙaryata ikirarin cewa gwamnatin tarayya na shirin mayar da wasu hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya zuwa Legas.
Ya bayyana haka ne ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, a wajen taron tunawa da Ahmadu Bello na shekara-shekara karo na 10, cewar rahoton The Punch.
Asali: Legit.ng