Hisbah Ta Kama Direbobin Adaidaita 52 Saboda Yin 'Askin Banza'
- Jami'an Hukumar Hisbah a jihar Kano sun yi nasarar kama wasu masu sana'ar adaidaita sahu akalla 52 saboda aikata ayyuka na rashin da'a yayin ayyukansu
- Ana zargin direbobin adaidaita sahun da aikata laifuka kamar cakuda maza da mata, yin askin banza, siya da sayar da miyagun kwayoyi da wasu abubuwa
- Mujahid Aminuddeen, mataimakin shugaban hukumar Hisbah na Kano, ya ja kunnen direbobin adaidaita sahun su zama jakadu nagari ga addinin musulunci a duk inda suke
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Kano - Hukumar Hisbah a jihar Kano ta sanar da cewa ta kama akalla direbobin adaidaita sahu 52 saboda samunsu da laifuka daban-daban da suka hada da askin banza, sayar da miyagun kwayoyi da kuma cakuda maza da mata a kekensu da suke sana’ar jigilar mutane.
Ana fargabar mutane 30 sun mutu yayin fada tsakanin sojoji da 'yan bindiga a jihar Arewa, bayanai sun fito
Jami’an Hisba sun kama direbobin ne a sassa daban-daban da ke birnin Kano kamar yadda The Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kwanakin baya bayan nan ne Hisbah din ta fitar da sanarwar cewa ta kaddamar da wani babban aiki mai taken ‘’ofireshon kau da badala’’ a yunkurin hukumar na kawo gyaran tarbiyya da kawar da miyagun dabi’u da suka hada da karuwanci, shaye-shaye, sayarwa da kuma kwankwadar barasa da sauransu.
Da yake jan kunnun direbobin su 52 a ranar Juma’a, Mujahid Aminuddeen, mataimakin shugaban hukumar Hisbah, ya bukaci su zama jakadu nagari ga addinin Musulunci da jihar Kano ta hanyar kauracewa dukkan wata badala.
A cewarsa:
‘’Muna son yin amfani da wannan dama domin yin roko a gareku da ku guji nuna dukkan wasu halaye da za su iya zubar da mutuncin addinin Musulunci da kuma kimar jihar Kano."
Wane irin laifuka masu adaidaita sahun suka aikata a Kano?
Ya kara da cewa laifukan da direbobin suka aikata sun hada;
‘’Askin banza, tuki a gari sanye da gajeren wando, amfani da hotuna da basu dace ba a jikin baburansu, cakuda maza da mata da kuma daukan ‘yan ta’adda zuwa wuraren da suke aikata miyagun laifuka.
‘’A matsayinmu na musulmai, ba zamu lamunci wannan halayya ta direbobin adadita sahun ba. Wannan ne kuma yasa kawo ku nan domin yi muku wa’azi akan illolin da ke tattare da wadannan ayyuka bisa tsarin addini da kuma al’adar mutanen jihar Kano.’’
Za mu cigaba da sa ido kan direbobi da suka ki daidaita sahunsu - Hisbah
A cewar mataimakin kwamandan, Hisbah za ta cigaba da sa ido domin tabbatar da cewa ta damko dukkan direbobin adadaita da suka ki daidaita sahunsu ta hanyar kin bin umarnin hukumar.
Rahotannni sun bayyana cewa an tattara direbobin da aka kama a hedikwatar Hisbah da ke birnin Kano inda manyan jami’an hukumar suka yi musu wa’azi kafin daga bisani a sallamesu.
An kashe rayuka sama da 30 yayin da kashe-kashen bayin Allah ya ci gaba da safiyar nan a jihar Arewa
Asali: Legit.ng