Yan Sandan Katsina Sun Aika Da Dan Bindiga Barzahu Yayin Harin Da Suka Kai Dandume

Yan Sandan Katsina Sun Aika Da Dan Bindiga Barzahu Yayin Harin Da Suka Kai Dandume

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta ce jami'anta sun yi nasarar hallaka wani mutum da ake zargin dan fashin daji ne
  • Abubakar Aliyu, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan na jihar Katsina ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar
  • Aliyu ya ce rundunar ta 'yan sandan ta gaggauta tura jami'anta zuwa garin na Dandume bayan samun rahoto kuma suka yi musayar wuta da bata-garin

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Katsina - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da cewa jami’anta sun hallaka wani mutum guda da ake zargin cewa dan bindiga ne a yayin da suka dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane a yankin Dandume da ke jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun yi musayar wuta da wadanda suka sace shugaban PDP, an rasa rai

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan jihar Katsina, Abubakar Aliyu, ya fitar a ranar Asabar ya bayyana cewa jami’ansu sun garzaya zuwa yankin bayan samun rahoton cewa ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari garin Dandume.

Yan sanda sun kashe dan bindiga a Katsina
Yan sanda sun dakile harin yan bindiga a Dandume a Katsina. Hoto: AUDU MARTE/AFP
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi musayar wuta tsakanin yan bindiga da yan sanda

Aliyu ya bayyana cewa rundunar ‘yan sanda ta gaggauta tura jami’anta zuwa garin tare da yin musayar wuta tare da ‘yan bindigar, rahoton The Cable.

kamar yadda sanarwar Kakakin rundunar ta bayyana:

“A ranar 25 ga watan Janairu da muke ciki da misalign karfe 7:30 na yammaci, babban ofishin rundunar ‘yan sanda da ke Dandume ya samu rahoton cewa an ga wata zugar ‘yan bindiga dauke da muggan makamai da suka hada da manyan bindigogi irinsu GMPG da Ak-47 sun nufo karamar hukumar Dandume."

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wani mai yin sojan gona a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar arewa

Sanarwar ta cigaba da cewa;

"Ba tare da wani bata lokaci ba bayan samun wannan sanarwa sai babban jami’in ofishin (DPO) ya ankarar da runduna ta musamman mai aikin tabbatar da zaman lafiya wacce ake kira ‘’Operation Sharan Daji’’ kuma kamar yadda aka sansu da rashin tsoro, sun tunkari ‘yan bindigar tare da yin musayar wuta da su.’’
‘’A sakamakon wannan gwabzawa, an samu gawar mutum guda da ake kyautata zaton yana daga cikin ‘yan bindigar tare da samun wata babbar bindiga mai dauke da sauran alburusai guda 27 masu tsawon 94.5mm a wurin da aka fafata musayar wuta’’.

Kwamishina ya yabawa jami'an 'yan sanda a Katsina

A cewar sanarwar ta Aliyu ya bayyana cewa kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Aliyu Abubakar Musa, ya yabawa jarumta, sadaukarwa, da kwarewar da jami’an rundunar ‘’Ofireshon Sharan Daji’’ suka nuna yayin fatattakar ‘yan ta’addar.

Kazalika, ya bayyana cewa kwamishinan ya bukaci jama’a da su cigaba da bawa rundunar ‘yan sanda hadin kai da goyon baya ta hanyar samar da bayanai akan al’amuran dukkan wasu ‘yan ta’adda da sauran miyagun jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel