Miyagun Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugaban Hukumar Gwamnati a Jihar PDP

Miyagun Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugaban Hukumar Gwamnati a Jihar PDP

  • Ƴan bindiga sun kutsa kai har cikin gida, sun yi awon gaba da shugaban tashohin motoci na jihar Oyo, Alhaji Akeem Akintola
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun sace babban mutumin ne da sanyin safiyar yau Asabar, 27 ga watan Janairu, 2024
  • Majiyoyi da dama sun tabbatar da faruwar lamarin amma har kawo yanzu rundunar ƴan sanda ba ta ce komai ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban hukumar kula da tashar Tipper, Lorry And Quarry Park na Jihar Oyo, Alhaji Akeem Akintola, wanda aka fi sani da Kuso.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an yi garkuwa da mutumin ne da sanyin safiyar Asabar, a kusa da unguwar Ajiboye, Omi Apata, Ibadan, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

An rantsar da Ododo matsayin sabon gwamnan jihar Kogi, wa'adin Yahaya Bello ya kare

Sufetan yan sanda na ƙasa, IGP Kayode.
Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Hukumar Kula da Tashar Oyo Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

A cewar wata majiya, maharan sun kutsa kai cikin gidan Akintola ba zato ba tsammani, inda suka yi awon gaba da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maharan sun shuga har cikin gida

Majiyoyi da dama sun tabbatar da faruwar lamarin, ciki har da wani dan uwa daga cikin iyalansa da abokan hulda da suka nemi kada a ambaci sunayen su.

A rahoton Leadership, majiyar ta ce:

"Ƴan bindigar sun kai farmakin ne da sanyin safiyar yau Asabar kuma kai tsaye suka tunkare shi ba tare da fuskantar wata turjiya ba daga bisani suka yi awon gaba da shi."

Rundunar ‘yan sandan jihar dai ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba har ya zuwa lokacin da muka haɗa maku wannan rahoton.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da lamarin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a sassan Najeriya. A kwanan nan ne aka yi garkuwa da shugaban PDP na jihar Legas.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe matar ɗan sanda da surukarsa a wata jihar Arewa

Ministan tsaro ya ce zasu binciki hafsan sojin ruwa

A wani rahoton na daban Bello Matawalle ya ce ma'aikatar tsaro zata gudanar da bincike kan zargin cin hanci da ake wa hafsan sojin ruwa.

Karamin ministan tsaro ya faɗi haka ne yayin martani kan wata badakala da aka bankaɗo ana zargin hafsan rundunar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262