Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mataimakin Shugaban Fitacciyar Jami'a a Najeriya

Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mataimakin Shugaban Fitacciyar Jami'a a Najeriya

  • Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin shugaban jami'ar ABSU, DVC Farfesa Godwin Emezue a jihar Abiya
  • Ganau sun bayyana cewa maharan sun tare Farfesan ne a gidan mai yayin da ya je shan mai a motarsa, suka tafi da shi zuwa inda ba a sani ba
  • Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan wasu tsageru sun yi awon gaba da shugaban jam'iyyar PDP na jihar Legas da wasu jiga-jigai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Umuahia, jihar Abia - Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin shugaban jami’ar jihar Abia (ABSU) da ke Uturu, (DVC) Farfesa Godwin Emezue.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an sace Emezue ne a wani gidan mai da ke kusa da Amachara, a yankin karamar hukumar Umuahia ta Kudu a jihar Abiya.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Ƴan bindigan da suka sace shugaban PDP na jiha sun aiko da saƙo mai ɗaga hankali

Yan bindiga sun sace mataimakin shugaban jami'ar ABSU.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mataimakin VC Na Jami'ar ABSU a Jihar Abia Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Farfesan ya je gidan man ne domin shan mai a motarsa tare da mai ɗakinsa yayin da ƴan bindigan suka cimmasa, suka yi awon gaba da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindigan suka sace DVC

Ganau sun shaida wa manema labarai cewa ƴan bindigar su uku, sun tare mataimakin shugaban jami'ar a wurin, suka tasa keyarsa zuwa cikin motar Lexus SUV jeep da suka aje a gefe.

Bayanai sun nuna cewa bayan sun ɗauki mutumin, ƴan bindigan sun bi hanyar iyakan jihar Imo da Abiya.

Har kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar ko rundunar ƴan sanda kan faruwar lamarin.

Yayin da aka tuntuɓi jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sanda reshen jihar Abia, ASP Maureen Chinaka, ba ta ɗaga kiran wayar salula ba kuma ba ta turo amsar sakonnin da aka aika mata ba.

Kara karanta wannan

Babban labari: An yi garkuwa da shugaban jam'iyyar PDP na jiha 1, sahihan bayanai sun fito

Yan bindiga sun sace shugaban PDP

Wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan wasu mahara sun yi garkuwa da shugaban jam'iyyar PDP na jihar Legas tare da wasu jiga-jigai da ke tare da shi.

Wani mamban jam'iyyar da ya nemi a sakaya bayansa ya ce masu garkuwan sun nemi N200m a matsayin kuɗin fansar jagororin PDP da suka sace.

An sassauta dokar kulle a Mangu

A wani rahoton kuma Gwamna Mutfwang na jihar Filato ya sassauta dokar zaman gida da ya ƙaƙaba dare da rana a ƙaramar hukumar Mangu

A wata sanarwa da kakakin gwamnan ya fitar ranar Jumu'a, ya ce a yanzu dokar zata riƙa aiki ne daga 4:00 na yamma zuwa 8:00 na safe

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262