Kakakin Majalisar Jihar APC da Aka Tsige Ya Nufi Kotu

Kakakin Majalisar Jihar APC da Aka Tsige Ya Nufi Kotu

  • Kakakin majalisar dokokin jihar Ogun da aka tsige, Olakunle Oluomo, ya tunkari kotu don kalubalantar wannan mataki na yan majalisa
  • Oluomo ya ce sauke shi da takwarorinsa 18 suka yi daga kujerarsa baya bisa ka'ida don haka yake neman kotu ta bi masa hakkinsa
  • Ya ce tun bayan rantsar da shi a kan wannan kujera a watan Yunin 2023, ne wasu takwarorinsa suka dauki karan tsana suka daura masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo, ya shigar da kara gaban babbar kotun jihar yana mai kalubalantar tsige shi da aka yi.

Mambobin majalisar jihar 18 ne suka tsige Olumo, mai wakiltar mazabar Ifo, a ranar Talata, yayin wani zama wanda mataimakiyar kakakin majalisa, Misis Bolanle Ajayi ta jagoranta.

Kara karanta wannan

Rundunar Soji ta tona asirin mutum 2 da ƙarin wasu abubuwa da suka jawo kashe-kashe a Filato

Kakakin majalisar Ogun da aka tsige ya tunkari kotu
Jihar Ogun: Kakakin Majalisa da Aka Tsige Ya Nufi Kotu Hoto: Olakunle Oluomo
Asali: UGC

Yan majalisa 18 cikin 26 ne suka tsige Oluomo, wanda hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta maka a gaban kotu, kan zargin badakalar kudade, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sauke shi daga kujerarsa ne kan zargin rashin da'a, girman kai, rashin alkibla da gaskiya, rashin iya shugabanci, almubazaranci da kudade da hada yan majalisa fada.

Na shigar da kara kotu, tsigaggen kakakin majalisar Ogun

Da yake martani kan ci gaban a ranar Juma'a, 26 ga watan Janairu, Oluomo ya bayyana tsige shi da aka yi a matsayin wanda baya bisa ka'ida.

Oluomo ya ce:

"Domin ku sani, na shigar da kara a babbar kotun jihar Ogun ina neman kotu ta tantance ko za a iya tsige kakakin majalisa ta hanyar juyin mulki.
"Kuma kotu ta ce a je a aika masu da sammaci wanda shine daidai sannan a dawo a ranar 7 ga watan Fabrairu don kare shari'armu.

Kara karanta wannan

Budurwa ta yi murnar shafe shekaru 5 ba tare da namiji ya kusanceta ba, mutane sun yi martani

"Ni mutum ne da ya yarda da tsarin doka wannan ne dalilin da yasa na nufi kotu."

Tun da aka zabe ni wasu takwarorina suka taso ni gaba, Oluomo

Ya yarda cewa tun da aka sake zabarsa a matsayin kakakin majalisar a watan Yunin 2023, bai sake samun goyon bayan majalisar ba, rahoton Trust Radio.

Olumo ya kara da cewar:

"Ba ni da matsala da takwarorina. Koda dai tun daga ranar farko, da na bayyana a matsayin kakakin majalisa a watan Yunin bara, tun lokacin, bana jin ta da dadi.
"Wasu yan majalisa wadanda basu so na zama kakakin majalisa ba daga wancan lokacin, sun ki daina farmaka na a majalisar. Ya kasance daga wannan matsalar zuwa wancan matsalar."

Dalilin tsige kakakin majalisar Ogun

A baya mun ji cewa mamba mai wakiltar mazaɓar Obafemi Owode a majalisar dokokin jihar Ogun, Soneye Kayode, ya bayyana maƙasudin tsige kakakin majalisar, Olakunle Oluomo.

A ranar Talata, ƴan majalisa 18 daga cikin 26 suka tsige kakakin majalisar dokokin jihar Ogun daga kan kujerarsa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng