Abun Bakin Ciki Ya Sake Faruwa a Ibadan Yayin da Gobara Ta Tashi a Ofishin INEC, An Yi Karin Bayani
- Ofishin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a karamar hukumar Ibadan ta Kudu maso Gabas ta kama da gobara
- Kwamishinan hukumar zabe na jihar, Dr Adeniran Tella, ya tabbatar da tashin gobarar a cikin wata sanarwa
- An tattaro cewa al'amarin ya afku ne da misalin karfe 10:30 na safiyar Juma'a, 26 ga watan Janairu, kasa da makonni biyu bayan faruwar wani mummunan al'amari a jihar
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Ibadan, jihar Oyo - Hukumar zabe a jihar Oyo ta tabbatar da tashin gobara a ofishinta da ke karamar hukumar Ibadan ta Kudu maso Gabas.
Wata sanarwa da Dr Adeniran Tella, kwamishinan zabe na jihar ya saki a garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ta bayyana cewa gobarar ta faru ne da misalin karfe 10:30 na safiyar Juma'a, 26 ga watan Janairu.
A karshe, rundunar sojin saman Najeriya ta nemi afuwar mutane kan kuskuren kashe bayin Allah a arewa
Yayin da har yanzu ba a tantance ainihin musabbabin tashin gobarar ba, ana hasashen cewa ta samo asali ne daga karfin wutar lantarki, kamar yadda kwamishinan zaben ya bayyana, rahoton PM News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya tabbatar da cewar ba a rasa rai ba sannan ya fayyace cewa kayan aiki kawai aka rasa.
Tella ya kara jaddada cewa lamarin ba zai yi tasiri a zaben mazabar Saki ta Yamma da za a yi a ranar 3 ga watan Fabrairu mai zuwa ba, rahoton Naija News.
Garin Ibadan ya yi fama da abubuwan bakin ciki da dama cikin kasa da makonni biyu, wanda na baya-bayan nan da ya afku shine tashin abun fashewa a yankin Bodija da ke garin wanda ya kai ga rasa rayuka da dukiyoyi.
Gobara ta lakume gidaje 50 a Benue
A wani labarin, mun ji cewa wata tsohuwa ƴar shekara 80 ta ƙone ƙurmus a wata gobara da ta ƙone gidaje 50 a ƙauyen Tse-Agubor Gyaruwa da ke gundumar Tsambee-Mbesev a ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma a jihar Benue.
Shugaban ƙauyen da abin ya shafa, Cif Ayatse Agubor, ya shaida wa manema labarai a Makurdi cewa, gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Lahadi, yayin da mutanen ƙauyen ke aiki a gonakinsu, cewar rahoton Daily Trust.
Asali: Legit.ng