Kotu Ta Yanke Hukuncin Daurin Rai da Rai Ga Malamin Addini Bisa Yi Wa Mabiyansa ‘Fyade’
- Kotun Tarayya da ke Legas ta yankewa wani Fasto daurin rai da rai kan zargin cin zarafi da kuma fyade
- Kotun ta yi hukuncin ne a yau Juma’a 26 ga watan Janairu inda ake zargin Fasto Feyi Daniels da aikata laifin
- Alkalin kotun, Rahman Oshodi ya yanke hukuncin ne bayan sauraran dukkan korafe-korafe da ke kansa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas – Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Legas ta yanke wa Fasto Feyi Daniels hukuncin daurin rai da rai.
Kotun ta yi hukuncin ne a yau Juma’a 26 ga watan Janairu inda ake zargin Faston da cin zarafi da kuma yi wa mamban cocinsa fyade.
Wane hukunci kotun ta yanke?
Hukumar kare cin zarafin ta DSVA ta kuma tabbatar da cewa an daure Daniels zaman gidan kaso har shekaru uku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
TheCable ta tattaro cewa wanda ake zargin ya musanta zargin da ake masa, kotun ta ba da umarnin daure shi a gidan kaso.
Mai Shari’a, Rahman Oshodi ya yanke hukuncin ne bayan sauraran dukkan korafe-korafe da ake tuhumarsa.
A watan Mayun 2023 an tsare Faston a kotu kan zargin haikewa mata ‘yar shekaru 25 a gidansa da ke Lekki.
Mamban cocin ta bayyana cewa Faston ya yi amfani da ita a lokacin addu’o’I a cocin, cewar The Guardian.
Mamban cocin ta ce Faston ya haike mata yayin da ya ke fadar wasu kalmomi wadanda ba ta fahimtar me ya ke nufi.
Shaidun da aka gabatar a kotun
Alkalin kotun ya ce masu gabatar da kara sun tabbatar da tuhume-tuhumensu kan Faston da zargin fyade.
Alkalin ya amince da shaidar wata mataimakiyar Faston da ya yi wa fyade a shekarar 2020.
Matar farko da Faston ya haike mata ta ce bayan ya sadu da ita ta kamu da ciwon sanyi inda ya bukace ta da shan magani.
Kotu ta yanke hukunci kan 'yan bijilanti 5
Kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Kano ta yanke hukunci kan wasu matasa 'yan bijilanti guda 5 a jihar.
Kotun ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya kan zargin hallaka wani matashi mai shekaru 17.
Mai Shari'a, Dije Audu Aboki ita ta jagoranci shari'ar tare da yanke hukuncin bayan sauraran tuhume-tuhumen.
Asali: Legit.ng