Miyagun Ƴan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari, Sun Kashe Bayin Allah Tare da Sace Wasu 29 a Arewa
- Miyagun ƴan bindiga sun kai hari kauyuka biyu a ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina, sun yi ajalin bayin Allah
- Rahoto daga mazauna yankin ya nuna cewa maharan sun sace mutane sama da 20 a hare-haren biyu da suka kai lokaci ɗaya
- Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Abubakar Aliyu, ya ce dakaru sun isa kauyukan domin kwantar da hankula da tabbatar da tsaro
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Mutum biyu sun mutu yayin da ƴan bindiga suka kai mummunan hari ƙauyukan Ɗan Alhaji da Ƴanɗaka da ke ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina.
Jaridar Punch ta rahoto cewa bayan kisan rayuka biyu, ƴan bindigan sun sace wasu mutane 29 a harin wanda suka kai ranar Talata da ta gabata.
Wasu majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa ƴan ta'addan sun kai harin ne lokaci guda kuma har zuwa jiya Alhamis babu wasu cikakkun bayanai kan ɓarnar da suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai an gano cewa ‘yan fashin dajin sun far wa kauyukan ne a lokaci guda, duk da tazarar da ke tsakaninsu.
Mazauna kauyukan sun bayyana cewa ɗaukin da jami'an tsaro suka kawo shi ne ya taƙaita ta'addancin da ƴan bindiga ka iya aikatawa kan jama'a yayin harin.
Wane mataki rundunar ƴan sanda ta ɗauka?
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Kakakin ƴan sandan ya ce:
"Lamarin biyu sun faru a lokaci guda a Dan Alhaji da kuma Yandaka. An kashe mutane biyu a harin yayin da muke da labarin cewa an yi garkuwa da mutane 29.
"Yanzu haka jami'an ƴan sanda suna can a kauyukan kuma suna ƙoƙarin shawo kan lamarin da dawo da zaman lafiya."
Garuruwa da dama a sassan ƙasar nan suna fama da hare-haren ƴan bindiga musamman Arewacin Najeriya, rahoton Leadership.
Amma duk da haka wani mazaunin Katsina ya faɗa wa Legit Hausa cewa tsaro ya ƙara inganta a faɗin jihar saboda matakan da gwamna mai ci ya ɗauka.
A cewar Malam Yusuf, ba zai yiwu a wayi gari a ce gaba ɗaya an daina kai hare-hare ba, abu ne da a hankali a hankali za a magance matsalar.
A kalamansa ya ce:
"Mun samu tsaro a Katsina, kuma idan ka yi duba zaka ga Batsari ne ake ɗan kai hari kuma su ma kaɗan-kaɗan, muna wa Dikko (gwamna mai ci) addu'a da ikon Allah zai kawo ƙarshen lamarin.
"Ban da Batsari, sauran yankunan da muke fama da ƴan ta'addan nan kamar Bakori, Ɗandume, yankin Funtua, Jibia da sauransu ai an samu tsaro, shiyasa ni a waje na zan ce an samu tsaro."
An kashe masu garkuwa 3 a Adamawa
A wani rahoton kuma tsagerun masu garkuwa da mutane 3 sun bakunci ƙahira yayin musayar wuta da ƴan sanda a jihar Adamawa
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, SP Suleiman .Nguroje, ya ce dakarun sun ceto mutum 3 da maharan suka sace.
Asali: Legit.ng