Filato: Asirin Wasu Mutane da Ake Zargi da Hannu a Kashe Bayin Allah Sama da 100 Ya Tonu a Arewa
- Jami'an ƴan sanda sun kama mutum 17 da ake zargin suna da hannu a kashe-kashen da ke faruwa a jihar Filato
- Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya nuna dukkan waɗanda aka kama a hedkwatar ƴan sanda a Jos
- Ya kuma bayyana irin hare-haren da dakarun ƴan sanda suka daƙile a wasu sassan jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Plateau - Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun cafke mutum 17 da ake zargi da kitsa hare-haren da suka laƙume rayukan bayin Allah a jihar Filato.
Rundunar ta ce mutum 17 da suka shiga hannu ana zarginsu da hannu a kai hare-haren jajibirin kirsimeti a kananan hukumomin Barkin Ladi da Bokkos da kuma na Mangu da aka yi kwanan nan.
Ɗaruruwan bayin Allah ne suka rasa rayukansu a waɗannan munanan hare-hare da aka kai, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin sufetan ƴan sanda na ƙasa mai kula da shiyya ta 4, Ebony Eyibio, shi ne ya bayyana waɗanda aka kama a hedkwatar ƴan sanda ta jihar Filato da ke Jos.
AIG Eyibio, wanda jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya wakilta, ya ce an kama mutum 9 da ake zargi da kitsa kashe-kashen baya bayan nan a Mangu.
Ya ce ƴan sanda sun kuma cafke ƙarin mutum 8 da ake zargin suna da alaƙa da kashe-kashen da aka yi a kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi ana gobe kirsimeti.
Yadda yan sanda suka dakile wasu hare-haren
Sai dai rundunar ƴan sandan ba ta bayyana sunaye da sauran bayanan waɗanda ake zargin ba.
A rahoton The Cable, kakakin ƴan sandan ya ce:
"A ranar 24/01/24 da misalin karfe 10:00 na dare muka samu bayanan sirri game da wani yunƙurin kai hari ƙauyen Ntam da Kamfanin ASTC, duk a karamar hukumar Mangu.
"Tawagar gwarazan dakarun ƴan sanda na rundunar IGP ta musamman da ke ASTC da haɗin guiwar kwamandan Pankshin da DPO suka yi gaggawar kai ɗauki kuma suka daƙile harin.
"Haka nan kuma ƴan sanda sun yi nasarar dakile yunƙurin wasu miyagu na cinna wuta a wuraren Ibada a yankin Panyam, dattawan yankin sun taimaka wajen daƙile lamarin."
Yan sanda sun ceto mutun 14 da aka yi garkuwa da su
A wani rahoton kuma Jami'an rundunar ƴan sanda na Abuja sun samu nasarar fatattakar ƴan bindiga tare da ceto mutum 14 da aka yi garkuwa da su.
Kwamishinan ƴan sandan FCT, CP Garba ya yabawa dakarun bisa wannan namijin ƙokari da suka yi a Operation ɗin.
Asali: Legit.ng