Kotu Ta Tura Yan a Mutun Gwamnan PDP Gidan Yari Kan Abu 1 Tak

Kotu Ta Tura Yan a Mutun Gwamnan PDP Gidan Yari Kan Abu 1 Tak

  • Tsugunne ba ta ƙare ba ga wasu magoya bayan gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara bayan sun gurfana gaban kotu
  • Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta ba da umarnin a tsaresu a gidan yari na Kuje
  • Ana dai zarginsu ne da hannu a kan fashewar wani abu a harabar majalisar dokokin jihar Rivers tare da ƙona ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja a ranar Alhamis ta bayar da umarnin tsare wasu magoya bayan gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara

Kotun ta bayar da umurnin ne bisa zarginsu da hannu a fashewar wani abu da ya auku a harabar majalisar dokokin jihar Rivers, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya aike da muhimmin sako ga Wike da Tinubu bayan nasara a Kotun Koli

Kotu ta tura magoya bayan Fubara gidan yari
Kotu ta aike da magoya bayan Gwamna Fubara zuwa gidan gyaran hali Hoto: @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

Fashewar dai da ta auku a harabar majalisar dokokin jihar a daidai lokacin da wasu ƴan majalisar suka yi yunƙurin tsige Gwamna Siminalayi Fubara a ranar 30 ga watan Oktoba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi zargin cewa wasu masu biyayya ga gwamnan ne suka haddasa lamarin.

Aƙalla mutum biyar daga cikinsu ne aka gurfanar da su a ranar Alhamis a gaban mai shari’a Bolaji Olajuwon na babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Sun haɗa da Chime Eguma Ezebalike, Prince Lukman Oladele, Kenneth Goodluck Kpasa, Osiga Donald da Ochueja Thanksgod.

Wane laifi ake tuhumarsu da shi?

A cikin tuhume-tuhume bakwai, ana zargin wadanda ake ƙarar da aikata laifukan ta’addanci ta hanyar kutsawa cikin majalisar dokokin jihar Rivers, yin ɓarna da ƙona majalisar a yayin rikicin siyasar da ya barke a Port Harcourt a watan Oktoban bara.

Kara karanta wannan

Kotu ta dauki mataki kan tsohon gwamnan da ake tuhuma da wawushe N4bn

An kuma zarge su da kashe Sufeto Bako Angbashim da wasu mutum biyar masu ba ƴan sanda bayani a yankin Ahoada na jihar.

A yayin zaman kotun na yau, Lukman Fagbemi, lauyan Chime Eguma Ezebalike da Prince Lukman Oladele, ya buƙaci kotun da ta bayar da belinsu saboda sun kasance a tsare a hannun ƴan sanda tun shekarar da ta gabata.

Jaridar The Nation ta ce lauyan gwamnati, Audu Garba, ya yi watsi da batun belin kan dalilin yanzu aka ba shi takardar neman belin kuma yana bukatar lokaci domin ya yi nazari a kai.

Wane hukunci alƙalin kotun ya yanke?

Mai shari’a Olajuwon ya amince da lauyan mai shigar da ƙara cewa neman belin da aka gabatar bai kai a saurare shi ba, ya kuma sanya ranar 2 ga watan Fabrairu domin sauraren dukkan buƙatun belin.

Har zuwa lokacin ci gaba da sauraren ƙarar da kuma yanke hukuncin neman belin, alƙalin kotun ya bayar da umurnin a kai waɗanda ake tuhuma gidan yarin Kuje, a tsare su kuma a dawo da su kotu a ranar da za a cigaba da sauraron ƙarar.

Kara karanta wannan

Zargin cin hanci: EFCC za ta binciki ‘dan siyasar da ya fi kowa dadewa a majalisa

Kotun Ƙoli Ta Tabbatar da Nasarar Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Gwamna Siminalayi Fubara a zaɓen gwamnan jihar Rivers na ranar 18, ga watan Maris, 2023.

Kotun ta sanya ƙafa ta yi fatali da ƙarar da jam'iyyar APC da ɗan takararta suka shigar suna ƙalubalantar nasarar da gwamnan ya samu a zaɓen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng