Babbar Nasara: Ƴan Sanda Sun Yi Kazamin Artabu da Ƴan Bindiga, Sun Ceto Mutane a FCT

Babbar Nasara: Ƴan Sanda Sun Yi Kazamin Artabu da Ƴan Bindiga, Sun Ceto Mutane a FCT

  • Jami'an rundunar ƴan sanda na Abuja sun samu nasarar fatattakar ƴan bindiga tare da ceto mutum 14 da aka yi garkuwa da su
  • Kwamishinan ƴan sandan FCT, CP Garba ya yabawa dakarun bisa wannan namijin ƙokari da suka yi a Operation ɗin
  • Ya kuma buƙaci mazauna birnin tarayya su kula da mutanen da ke shiga cikinsu kuma kar su ɓata lokaci wajen kai rahoton wanda ba su aminta da shi ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Jami'an ƴan sanda na sashin yaƙi da masu garkuwa da mutane reshen Abuja sun samu nasarar ceto mutum 14 da ƴan bindiga suka sace.

Dakarun ƴan sanda sun samu wannan nasara ne yayin da suka kai samame maɓoyar masu garkuwa a kauyen Ukya da ke kusa da bodar jihar Nasarawa ranar Laraba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da yawa sun baƙunci lahira yayin da suka kai hari a jihar arewa, mutum 2 sun tsira

Yan sanda sun samu nasara a Abuja.
Dakarun Yan Sanda Sun Ceto Mutum 14, Sun Halaka Masu Garkuwa a Abuja Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Bayan samun sahihan bayanan sirri, dakarun yaƙi da garkuwa da jami'an ƴan sanda na hedkwatar Rubochi suka haɗu suka kutsa kai sansanin ƴan bindiga a Ukya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton Channels tv ya nuna cewa ƴan sanda na karisawa wurin, miyagun suka buɗe musu wuta, suka maida martani wanda ya sa aka yi kazamin artabu.

Yayin wannan musayar wuta ne, jami'an tsaron suka halaka ɗaya daga cikin masu garkuwa yayin da sauran suka tsere zuwa cikin jeji ɗauke da raunukan harbi.

Bayan haka sun ceto waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya kuma tuni aka sake miƙa su ga iyalansu cikin farin ciki da sam-barka.

Yan sanda sun lashi takobin kawar da tsageru

Kwamishinan ‘yan sandan FCT, CP Haruna G. Garba, ya nanata kudurinsa na kawar da duk wani nau’i na miyagun laifuka a Abuja da kuma tabbatar da zaman lafiya ga daukacin mazauna birnin.

Kara karanta wannan

Filato: Asirin wasu mutane da ake zargi da hannu a kashe bayin Allah sama da 100 ya tonu a Arewa

Ya kuma yaba tare da jinjinawa gwarzontaka da jajircewar dakarun ƴan sandan da suka kai wannan samame kuma aka samu nasara, rahoton Daily Post.

CP Garba ya kuma buƙaci mazauna birnin su yi taka tsan-tsan da mutanen da ke kewaye da su kana su gaggauta kai rahoton duk wani motsi da ba su yarda da shi ba.

Boko Haram ta yi wa sojoji ɓarna

A wani rahoton kuma Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun mamayi dakarun sojin Najeriya, sun buɗe musu wuta a jihar Borno.

Wata majiya daga cikin sojojin ta ce ƴan ta'addan sun kashe soja ɗaya da wasu jami'an tsaro biyu a harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262