“Gani Miloniya Kuma Na Mallaki Gidan Mai a Shekaru 24”: Matar Aure Ta Fada ma Duniya Nasarorinta
- Wata matashiya ta fito don fada ma mutane abubuwan da ta cimmawa a rayuwarta duk da cewar shekarunta 24 kacal a duniya
- A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, matashiyar ta ce tana da aure kuma ta mallaki gidan mai da ke aiki a yanzu haka
- Ta ce ita miloniya ce, ta mallaki mota, shago, gida sannan kuma ta kammala karatunta na digiri duk da kuruciyarta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wata matashiya yar Najeriya ta fito ta sanar da mabiyanta na soshiyal midiya tarin nasarorin da ta samu a rayuwa.
A wani bidiyo da @fumy_layor ta wallafa, matashiyar ta bayyana karara cewa ta cimma abubuwa masu tarin yawa a shekaru 24 a duniya.
Ta ce ta mallaki gidan mai, mota, sannan ta kammala karatunta na digiri, bugu da kari ita matar aure ce kuma mai gidan kanta duk a shekarunta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matashiyar ta kuma ce ita din miloniya ce amma bata bayyana yawan miliyoyin da ke a cikin asusunta na banki ba.
Ta rubuta:
"Matar oga, mai digiri, mai shago, miloniya, mai mota kuma mai gidan kanta a shekaru 24."
A halin da ake ciki, mutane da dama sun yi martani kan bidiyon inda mata da dama suka garzaya sashin sharhi don bayyana nasu nasarorin da shekarunsu.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@Ugegbe Oyibo ta ce:
"Nima gida, biloniya, matar aure da yara. da GLK kamar guda biyu a shekaru 19. Kada ku yarje ma kowa. Ba ni za ku dagawa hankali ba."
@_amaka_amaka ta yi martani:
"Nima matar oga a shekaru 19, na kammala karatu a shekaru 19, yar kasuwa a 19, mai gida a 19, mai gida a 19, uwar yara biyar a 19 kuma mai jirgin sama."
@Favour Kalu ta ce:
"Na yi amfani da kudina wajen siyar wayata."
@KingBless ta ce:
"Kada ka yarje ma kowa a shekarar nan ta 2024."
Jarumar fim tace Baturiya take so ta zama a gaba
A wani labarin kuma, jarumar fina-finan Kudu wato Nollywood, Destiny Etiko, ta bayyana cewa idan har Allah zai sake halitto ta a wata rayuwar, toh a baturi take so ta zo.
Jarumar ta bayyana hakan ne yayin da take martani ga wani bidiyo da mai watsa shirye-shirye ta Instagram, Tunde Ednut ya wallafa, inda ya yan mata biyu dake bayani kan yancin cin gashin kansu, rahon Daily Trust.
Asali: Legit.ng