Dan Takarar Gwamnan LP Ya Biya Bashin da Matarsa Ta Ci Bayan An Sha Yar Dirama a Twitter
- A karshe Gbadebo Rhodes-Vivour ya biya albashin da wani mai amfani da dandalin X, Chika Jones ke bin matarsa, Ify bayan an sha wata yar dirama a Twitter
- Daga Chika har Rhodes-Vivour sun tabbatar da biyan bashin a shafukansu na X a ranar Talata, 23 ga watan Janairu
- Da farko tsohon ma'aikacin na matar Rhodes-Vivour ya yi zargin cewa an rike masa albashinsa tsawon watanni takwas ba tare da an biya shi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Abuja - Dan takarar gwamna na jam'iyyar LP a zaben 2023 da aka yi a jihar Legas, Gbadebo Rhodes-Vivour, ya biya albashin da wani mai amfani da dandalin X, Chika Jones, ke bin matarsa Ify.
Chika, wanda ya yi aiki a matsayin marubuci kuma mai kula da kamfanin Afroscientric.com, mallakin Ify Rhodes-Vivour ya tabbatar da samun kudin nasa bayan da dan takarar na LP ya neme shi.
Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @chika_jones, a ranar Talata, 23 ga watan Janairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mafarin al'amarin Chika da Ify
Da farko dai ya yi zargin cewa an rike masa albashin watanni takwas a lokacin da yake yi wa Ify aiki.
Da yake tabbatar da biyan albashin, ya rubuta:
"Na samu biyan kudi daga #GRVlagos. Ga hoton biyan kudin a nan.
"Karin bayani na karshe kan wannan. #GRVlagos ya biyani. Na gode masa da ya dau mataki a wannan mawuyacin yanayi. An biya bashin."
Rhodes Vivor ma ya tabbatar da cewar an magance lamarin kuma an biya Chika hakkinsa.
Da yake rubuta hakan a dandalinsa na X, ya ce:
"An magance lamarin kuma an biyasa bashin da yake bi. Sannan ina so na nuna godiyata ga duk wadanda suka bayar da goyon bayansu a wannan lamari.
"Ina godiya ga Chika bisa fahimtyarsa da shirin mantawa da komai sannan kuma ina gode masa kan goyon bayansa a lokacin yakin neman zaben."
An gurfanar da Dan Bilki a kotu
A wani labarin, mun ji cewa kotun Majistare da ke Kano ta tsare Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda kan kalaman batanci ga Sanata Rabiu Kwankwaso.
Kotun ta tsare fitaccen dan siyasar ce kan kalaman nasa wadanda suka kasance barazana ga tsohon gwamnan da kuma neman ta da husuma a jihar.
Asali: Legit.ng