Yan Bindiga Sun Kwashi Kashinsu a Hannun Dakarun Sojoji, an kashe su da dama a jihar arewa
- Sojojin Najeriya sun samu nasarar ceto wasu mutane huɗu da aka yi garkuwa da su a jihar Kebbi ranar Litinin
- Mai magana da yawun Gwamna Idris ya ce sojoji tare da taimakon ƴan banga sun ragargaji ƴan bindigan, sun kwato muggan makamai
- Ya ce sojoji sun samu wannan nasara ne a kauyen Sabon Birni da ke ƙaramar hukumar Shanga a jihar Kebbi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Dakarun sojojin Najeriya da haɗin guiwar 'yan banga sun samu nasarar ceto wasu mutane hudu da 'yan bindiga suka yi garkuwa a jihar Kebbi ranar Litini.
Rahoton The Nation ya nuna cewa ƴan bindigan sun sace mutanen ne daga kauyen Sabon Birni da ke karamar hukumar Shanga a jihar, amma sojoji suka kwato su.
Mai magana da yawun Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi, Malam Yahaya Sarki, ne ya bayyana wannan nasara da sojoji suka samu a Birnin Kebbi ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce mutanen huɗu da suka ƙunshi maza uku da mace ɗaya, an ceto su cikin ƙoshin lafiya kuma tuni aka sake haɗa su da iyalansu, Vanguard ta tattaro.
Yan bindiga sun kashi kashinsu a hannun sojoji
Dakarun sojin Bataliya ta 1 na barikin Dukku a yankin Birnin Kebbi tare da haɗin guiwar ƴan banga ne suka kai samame kauyen Sabon Birni ranar Litinin da ta gabata.
Hadimin gwamnan ya ce:
"Tawagar jami'an tsaron sun ragargaji tare da kashe wasu yan bindiga kana suka lalata sansanin su. Sun kuma kwato bindigu ƙirar AK-47 guda uku maƙare da harsasai.
"Haka nan sun ƙwato alburusai 142, da kakin sojoji da dai wasu kayayyaki daga hannun ƴan ta'addan."
Ya ƙara da cewa mutane 4 da gwarazan sojojin suka ceto sun haɗa da Alhaji Hakimi Rumbu da Amina Dikko ƴan asalin kauyen Sangara a karamar hukumar Shanga.
Sauran sune Alhaji Abdullahi da kuma Bello Abdullahi ƴan kauyen Tungan Namuna a karamar hukumar Koko/Besse duk a jihar Kebbi.
Yan bindiga sun yaudari mutane a Katsina
A wani rahoton na daban Yan bindiga sanye da kakin soji sun yi awon gaba da bayin Allah sama da 30 a yankin ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina.
Wata majiya daga yankin ta ce maharan sun yaudari jama'a da sunan jami'an tsaro ne aka turo su ba su kariya.
Asali: Legit.ng