Mummunar Gobara Ta Lakume Kayayyakin Miliyoyin Naira a Fitacciyar Kasuwar Jihar Arewa
- An samu tashin wata mummunar gobara a kasuwar yan waya da ke a birnin Damaturu na jihar Yobe
- Gobarar wacce ta tashi cikin dare dai ta jawo asarar dukiya mai tarin yawa bayan ta ƙone shaguna 30 a kasuwar
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihr wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce za a gudanar da bincike don tantance yawan ɓarnar da gobarar ta yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Yobe - Shaguna da dama da dukiyoyi na miliyoyin Naira ne suka lalace a daren ranar Litinin bayan da gobara ta tashi a kasuwar waya ta Damaturu a jihar Yobe.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa gobarar wacce ta tashi da misalin ƙarfe 6:23 na dare, ta ɗauki sa'o'i kafin a samu damar kashe ta.
Jami'an tsaro, ƴan kwana-kwana da jama'ar yankin ne dai suka yi haɗin gwiwa wajen kashe gobarar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kasuwar wacce aka fi sani da Kasuwar Jagwal tana a unguwar Abashawa cikin birnin Damaturu, babban birnin jihar, inda ta samar da wuraren kasuwanci ga dubban ƴan kasuwa da masu sana’ar hannu a yankin.
Me hukumomi suka ce kan gobarar?
DSP Dungus Abdulkarim, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Yobe, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce ba tare da ɓata lokaci ba aka aike da jami’an tsaro da motocin kashe gobara zuwa wurin.
A kalamansa:
"Gobarar wacce ta tashi da karfe 6:23 dare, ta yi sanadiyar ƙona shaguna sama da talatin. An yi sa'a, ba a rasa rayuka a lokacin da lamarin ya faru ba.
"Ƴan kwana-kwana sun kula da gobarar, yayin da sama da shaguna 30 suka ƙone gaba daya."
Ya ƙara da cewa za a gudanar da cikakken bincike domin sanin girman ɓarnar da gobarar ta yi.
Yadda gobarar ta tashi
Wani shaidar ganau ba jiyau ba, mai suna Baba Musa, ya ce gobarar ta tashi ne a ɗaya daga cikin shagunan, sannan ta laƙume sauran shaguna a kasuwar.
Musa wanda ke sana’ar sayar da wayoyin hannu ya koka kan yadda wasu ƴan kasuwa suka yi asarar kayayyakinsu a gobarar.
An dai baza jami’an tsaro a kasuwar domin hana ƴan baranda satar kayayyaki.
Gobara Ta Tashi a Kasuwar Panteka
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin wata mummunar gobara a kasuwar Panteka da ke jihar Kaduna.
Gobarar wacce ta shafi ɓangaren ƴan katako na kasuwar ta jawo asarar miliyoyin naira ga ƴan kasuwa.
Asali: Legit.ng