Dangote Ya Samu Kazamar Riba Cikin Sa'o'i 24 Yayin da Kamfaninsa Ya Kafa Sabon Tarihi

Dangote Ya Samu Kazamar Riba Cikin Sa'o'i 24 Yayin da Kamfaninsa Ya Kafa Sabon Tarihi

  • Arziƙin attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, Aliko Dangote ya sake ƙaruwa cikin sa'o'i 24 da suka gabata
  • Bayanai na baya-bayan nan sun nuna cewa Dangote ya samu sabon matsayi a cikin attajiran duniya bayan ya samu sama da N760bn
  • Sabon arziƙin da Dangote ya samu ya samo asali ne sakamakon taka rawar ganin da kamfanin simintin Dangote ya yi a kasuwar hada-hadar kuɗi ta Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, Aliko Dangote, ya ƙara yawan arziƙinsa tare da tabbatar da matsayinsa a cikin manyan attajirai na duniya.

A cewar ƙididdigar mujallar Forbes, dukiyar Dangote ta haura dala miliyan 853 (N760.03bn) a ranar Litinin, 22 ga watan Janairu, 2023, inda ta kai dala biliyan 17.8.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta lakume kayayyakin miliyoyin naira a fitacciyar kasuwar jihar Arewa

Arzikin Dangote ya karu da N760bn
Cikin sa'o'i 24 arzikin Dangote ya karu da N760bn Hoto: Anadolu Agency
Asali: Getty Images

Hakan na nufin a cikin kwanaki 23 da suka gabata Dangote ya samu dalar Amurka biliyan 7.5 kwatankwacin Naira tiriliyan 6.8, duba da yadda ya fara sabuwar shekara da dala biliyan 10.3.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa arziƙin Aliko Dangote ke ƙaruwa?

Yawan ƙaruwar arzikin Dangote ya nuna tagomashin da kamfanoninsa suke samu a kasuwar hada-hadar ƙuɗi ta Najeriya.

Kamfanin siminti na Dangote, wanda shi ne kamfanin da yafi kawo wa Dangote kuɗi, darajar hannun jarinsa ta haura kaso 85.3%, inda ya kai N592.60 a ranar Litinin daga N337.10 da ya fara shekarar da shi a ranar 9 ga watan Janairun 2024.

Jarin kamfanin simintin Dangote ya kuma haura Naira tiriliyan 10 a ranar Litinin, 22 ga watan Janairu, inda ya zama kamfani na farko a Najeriya da ya samu wannan matsayi.

Kara karanta wannan

Abdulsamad Rabiu ya samu sabon matsayi a jerin attajiran duniya bayan ya zarce Mike Adenuga

Hakazalika, kamfanin sikarin Dangote, ɗaya daga cikin kamfanoninsa da ke a kasuwar hada-hadar kuɗi ta Najeriya, a halin yanzu shi ne na 13 mafi daraja a kasuwar.

Jarin kamfanin sikarin na Dangote dai yanzu ya kai Naira biliyan 960 a kasuwar hada-hadar kuɗi ta Najeriya.

Hakazalika farashin hannun jarin kamfanin sikarin ya ƙaru da kaso 38.6%, inda ya kai N79.00 kan kowane hannun jari ɗaya idan aka kwatanta da N67.80 da ya fara da shi a wannan shekarar.

Arzikin Abdulsamad Rabiu Ya Ƙaru

A wani labarin kuma, kun ji cewa Abdulsamad Rabiu mai kamfanin BUA, ya samu sabon matsayi a cikin jerin attajiran Najeriya.

Hamshaƙin attajirin ya koma na biyu cikin attajiran Najeriya bayan ya doke Mike Adenuga mai kamfanin sadarwa na Globacom.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng