Rashin Tsaro: Ministan Tinubu Ya Bayyana Wadanda Ke Daukar Nauyin Yan Bindiga a Najeriya
- Asirin masu daukar nauyin ta'addanci ya fara tonuwa yayin da Ministan Tinubu ya daga yatsa ga manyan kasar
- Ministan ma'adinai a Najeriya, Dele Alake ya bayyana cewa manyan kasar masu karfin iko ke daukar nauyin ta'addanci
- Alake ya ce hakar ma'adinai wanda ke jawo rashin tsaro sosai a fadin kasar ana yi ne ba bisa ka'ida ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Minsitan Ma'adinan Kasa, Dele Alake ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta himmatu wurin samar da tsaro a kasar.
Alake ya na magana ne kan hakar ma'adinai wanda ke jawo rashin tsaro sosai a fadin kasar inda ya ce za su dakile hakar ba bisa ka'ida ba.
Mene Ministan Tinubun ke cewa?
Ministan ya ce akwai wasu manyan mutane a Najeriya da suke daukar nauyin ta'addanci da ke da alaka da hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dele ya bayyana haka ne a Ibadan yayin kai ziyarar jaje bayan abin fashewa ya jawo rasa rayuka da asarar dukiyoyi a jihar, cewar Daily Trust.
Ya ce mafi yawan matsalar tsaron ta ta'allaka ne ga hakar ma'adinan ba bisa ka'ida ba wanda masu iko ke cin gajiyarshi a kasar.
Wace shawara Ministan Tinubun ya bayar?
A cewarsa:
"Akwai matsaloli da dama dangane da hakar ma'adinai musamman wanda ake yi ba bisa tsari ba.
"Amma Gwamnatin Tarayya ta na aiki tare da jihohi da kananan hukumomi da kuma yankuna da suke da masaniya kan yanayin tsarin wurin zamansu.
"Hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba ya danganci dukkan matakan al'umma ne, muna kokarin samar da hanyoyin dakile matsalar baki daya."
Alake ya kuma shawarci 'yan Najeriya da su rinka kai rahoton duk wata matsala a yankunansu da ba su amince da ita ba.
Ya ce rashin kai rahoton da wuri shi ke dagula lamarin yadda ba za a kawo karshen abin cikin sauki ba, cewar Tribune.
Tinubu ya fadi dalilin samar da Ministoci 47
Kun ji cewa Shugaba Tinubu ya bayyana dalilinsa na kin rage yawan Ministoci a Najeriya.
Tinubu ya ce rage ma'aikatun da kuma daurawa wasu nauyin ba zai taba samar da abin da ake nema ba.
Asali: Legit.ng