Tashin Hankali Yayin da Wata Mata Ta Jefa Jaririnta Cikin Kogi, Yan Sanda Sun Dauki Mataki
- Wata mata ta yi yunƙurin salwantar da ran jaririnta mai watanni biyar a duniya bayan ta jefa shi cikin wani kogi a jihar Ogun
- Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da cafke matar wacce take da shekara 30 a duniya bayan wannan mummunan yunƙuri da ta yi
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar wacce ta tabbatar da lamarin ta bayyana cewa an ceto jaririn kuma yanzu haka ya dawo cikin hayyacinsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ogun - Rundunar ƴan sandan jihar Ogun ta ce jami’anta sun kama wata mata mai Olubunmi Ajayi mai shekara 30, bisa yunƙurin nutsar da jaririnta mai watanni biyar, mai suna Imole Anifowose a kogin RSS, da ke Sagamu.
An bayyana cewa wani mutum mai suna Olusola Sonaya da ke kusa da kogin, ya taimaka wajen ceto jaririn bayan mahaifiyarsa ta jefa shi cikin kogin, cewar rahoton The Punch.
Jaridar Daily Trust ta ce hakan ya fito ne daga wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Omolola Odutola, ta aikewa manema labarai a ranar Litinin, 22 ga watan Janairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane hali jaririn yake ciki?
An garzaya da jaririn zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Olabisi Onabanjo da ke Sagamu domin kula da lafiyarsa.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"An garzaya da jaririn zuwa asibitin OOUTH domin a kula da lafiyarsa cikin gaggawa, inda daga baya ya dawo cikin hayyacinsa."
"An cafke mahaifiyar kuma a halin yanzu ana duba ta don tabbatar da lafiyar kwakwalwarta. An yi ƙoƙarin tuntuɓar dangi ko mijinta don miƙa musu jaririn su ci gaba da ba shi kulawa yadda ya dace."
Matar Aure Ta Yi Yunkurin Halaka Ɗiyar Makwabcinta
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata matar aure ta jefa wata ƙaramar yarinya cikin wani mawuyacin hali, bayan ta yi yunƙirin salwantar da ranta har lahira.
Matar auren dai ta daɓa wa yarinyar wuƙa a cikinta inda ta taso ta halaka ta domin ɗaukar fansa kan abin da mahaifin yarinyar yake yi, na ba mijinta shawarar ya yi mata kishiya.
Asali: Legit.ng