Rikici Tsakanin Boko Haram Da ISWAP Ya Yi Ƙamari Yayin Da Suka Kashe Juna a Sabon Rikici
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Jihar Borno - Kazamin rikici tsakanin mayakan Boko Haram da tsaffin abokan huldarsu, Islamic State of the West African Province (ISWAP) a Tafkin Chadi, na cigaba da yin kamari inda aka kashe da dama a bangarorin biyu.
Sabon rikicin wanda ya fara a ranar Asabar ya cigaba har zuwa ranar Lahadi 21 da watan Janairu, ya samo asali ne yayin da tawagar jiragen ruwan Boko Haram takwas dauke da mayaka 15 suka kai wa ISWAP hari a Tumbin Jaki, Jihar Borno.
Zagazola Makama ya rahoto cewa harin ramuwar gayya ne kan harin da ISWAP ta kai ranar 15 ga watan Janairu a sansanin Abou Hurayra, shugaban Boko Haram tsagin Buduma da ke Tsibirin Kaduna Ruwa a Tafkin Chadi kusa da Karamar Hukumar Kukawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun ce an kashe mayakan ISWAP da dama yayin da wasu kuma suka tsere saboda tsoron kada a kashe su a filin daga.
Majiyoyi sun rahoto cewa harin na baya-bayan nan an kai shi ne da nufin farautar Ali Kwaya da Abu Hussaini da wasu mayaka da ke boye a kusa da Tumbum Jaki, Tumbun Kanta, Mangari da Kaikura inda ISWAP ke da iko.
Hakazalika, wasu majiyoyin sun ce tuni ISWAP ta kwashe fursunoninta daga Jubularam zuwa wani boyayyen wurin a Tumbum Naira saboda fargabar tsagin Boko Haram zai iya kawo musu hari a sansaninsu.
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng