Tashin Hankali Yayin da Gobara Ta Cinye Tsohuwa Mai Shekaru 80 a Jihar Benue

Tashin Hankali Yayin da Gobara Ta Cinye Tsohuwa Mai Shekaru 80 a Jihar Benue

  • Wata tsohuwa mai shekaru 80 ta kone har lahira a karamar hukumar Gwer West da ke jihar Benue bayan tashin gobara
  • Matar mai yawan shekaru ta mutu saboda babu wanda ya kasance a kusa da ita a lokacin da gobarar ta tashi
  • Shugaban kauyen, Cif Ayatse Agubor, ya ce gobarar ta auku ne sakamakon kona daji da ba bisa ka’ida ba

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Gwer West, jihar Benue – Wani bala’i ya afku a ranar Lahadi, 21 ga watan Janairu yayin da wata gobara ta cinye wata mata ‘yar shekaru 80 a duniya a Tse-Agubor Gyaruwa da ke gundumar Tsambee-Mbesev a karamar hukumar Gwer West a jihar Benue.

Kara karanta wannan

An shiga mummunan yanayi a Legas, gobara ta yi kaca-kaca da wani bene mai hawa 10

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, gobarar da ta tashi ne da misalin karfe 10 na safe, inda ta kone gidaje 50 a yankin.

Mata ta kone kurmus a gobarar da ta tashi a jihar Benue
Yadda tsohuwa ta mutu a gobarar jihar Benue | Hoton nan ba ya nuna inda lamarin ya auku bane, nuni yake ga misalin yadda gobara ke cinye wuri
Asali: Getty Images

Shugaban kauyen, Cif Ayatse Agubor, ya ce tsohuwa ‘yar shekara 80 bata samu wanda ya taimaka mata bane a a lokacin da wutar ta kama, wannan yasa ta mutu a ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe wannan bati ya fito?

Agubor ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Makurdi, babban birnin jihar.

Hakimin kauyen ya bayyana cewa gobarar ta faru ne sakamakon kona daji da wasu ke yi ba tare da izinin hukumomi ba.

Ya gargadi matasan yankin da su daina wannan aika-aika na kone daji ko kuma su fuskanci fushin doka.

Yadda wata mata ta yi asarar dukiya

Daya daga cikin mazauna kauyen, Hajia Kongo ta ce ta yi asarar sama da buhu 10 na masara da waken soya da tufafi da sauran kayayyakin gida da suka hada da kudi Naira 110,000, Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wata mata ta sheke abokin 'sharholiyarta' bayan da ya nemi karin lalata da ita

Kongo ta bayyana cewa ta boye kudin ne a cikin buhunan masarar da suka kone. Ta roki daidaikun mutane da gwamnati da su kawo mata dauki sakamakon barnar da gobarar ta yi mata.

Gobara ta tashi a wani yankin Legas

A wani labarin kuma, wani gini mai hawa 10 da ke kan titin Broad a karamar hukumar Legas Island a jihar Legas ya kama da wuta.

Daraktar hukumar kashe gobara ta jihar Legas, Margaret Adeseye ce ta bayyana hakan ga jaridar Punch a ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.