Tsadar Rayuwa: Jihohi 10 Da ’Yan Najeriya Ke Shan Tsada Wajen Siyar Gas Din Girki
- ‘Yan Najeriya sun sake gamuwa da karin farashin gas din girki yayin da farashinsa ya tashi sama da yadda aka saba siya a kasuwa
- Wasu sabbin bayanai daga hukumar NBS sun bayyana cewa, an samu karin 8.70% a gas mai nauyin 12.5k sai kuma Karin 12.31% a mai nauyin 5kg
- Bincike ya nuna yankunan Arewa maso Gabas ne suka fi fuskantar tsadar gas din girki a yayin da farashin kayayyaki ke kara hawa
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Hukumar kididdiga ta Najeriya (NBS) ta bayyana sabon farashin iskar gas din girki da ‘yan Najeriya ke siya a kasuwa.
A cewar rahoton, ‘yan kasar sun ga Karin farashi sabanin yadda suka saba siya a kasuwanni a lokutan bayan kadan da suka gabata.
Yadda kididdigar take
Legit ta naqalto daga NBS cewa, 5kg na gas din girki ya samu Karin akalla 2.79% a matakin wata-wata daga N4,828.18 a watan Nuwamban 2023 zuwa N4,962.87 a watan Disamban 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A matakin shekara-shekara, 5kg na gas ya karu da 8.70% daga N4,565.56 a watan Disamban 2022.
Rahoton ya bayyana cewa, gas mai nauyin 12.5kg ya samu karin 3.18% a matakin wata-wata, daga N11,155.15 na watan Nuwamban 2023 zuwa N11,510.16 a watan Disamban 2023.
A matakin shekara-shekara, gas mai nauyin 12.5kg ya karu da 12.31% daga N10,248.97 a watan Disamban 2022.
Jihohin da aka fi tsadar da arahar gas
A cewar NBS, jihar Adamawa ce ta fi kowacce jiha tsadar iskar gas, inda ake siyar da 5kg a farashin N5,725.33 sai kuma Jigawa da ake siyar da gas din N5,686.88 da kuma Legas mai N5,671.05.
A gefe guda, jihohin da aka fi arahar gas sun hada da Ebonyi da ake samun 5kg a N4,071.43 sai kuma Imo da Abia N4,088.24 and N4,155.88 bi da bi.
Jihohi 10 da aka fi tsadar gas
- Cross River - N13,572
- Edo - N13,265
- Delta - N13,041
- Jigawa - N12,909
- Benue - N12,720
- Kogi - N12,700
- Nasarawa - N12,445
- Ekiti - N12,556
- Yobe - N12,000
- Kwara - N11,992
Jihohin da suka fi arahar man fetur
A wani labarin, kididdigar hukumar NBS ta bayyana alkaluman farashin man fetur a Najeriya da yadda aka siyar dashi zuwa karshen watan Disamban bara; 2023.
A cewar kididdigar, an siyar da man fetur a kan farashin N671.86 a watan Disamban shekarar da ta gabata ta 2023.
Asali: Legit.ng