An Shiga Mummunan Yanayi a Legas, Gobara Ta Yi Kaca-Kaca da Wani Bene Mai Hawa 10

An Shiga Mummunan Yanayi a Legas, Gobara Ta Yi Kaca-Kaca da Wani Bene Mai Hawa 10

  • Wani rahoto ya bayyana yadda wata gobara ta yi kaca-kaca da wani katafaren gini a jihar Legas da ke Kudu maso Yamma
  • An ruwaito cewa, gobarar ta kuma kama ginin Mandilas dake jihar, inda har yanzu ake ci gaba da aikin agaji
  • Jihar Legas na daga cikin jihohin da ake yawan fuskantar haddura irin wadannan na gobara ko rushewar ginin bene

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Jihar Legas - Wani gini mai hawa 10 da ke kan titin Broad a karamar hukumar Legas Island a jihar Legas ya kama da wuta.

Daraktar hukumar kashe gobara ta jihar Legas, Margaret Adeseye ce ta bayyana hakan ga jaridar Punch a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Wata mata ta sheke abokin 'sharholiyarta' bayan da ya nemi karin lalata da ita

Gobara ta kama a wani ginin Legas
Yadda gobara ta kama a wani yankin Legas| Hoto: @Mr_JAGs
Asali: Twitter

Gobarar da har yanzu ba a tantance musabbabin tashinta ba ta rutsa da shahararren ginin Mandilas da ke yankin tun daga hawa na farko na ginin har ta zarce zuwa hawa na hudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Margaret ta bayyana cewa, a yanzu haka jami’an ba da agajin gaggawa daga hukumomin kashe gobara na Ebute Elefun da Sari Iganmu na can a wurin domin dakile ci gaba da ta’azzararta.

Hadimin gwamna ya tabbatar da faruwar hakan

Wani karin haske da Jubril Gawat, mai hadimin gwamnan jihar ya bayyana kadan daga abin da ya faru.

Ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa:

"Tsohon ginin Mandilas da ke titin Broad a tsibirin Legas. Jami'an hukumar kashe gobara ta Legas, 'yan sandan Najeriya da tawagar ba da agajin gaggawa da sauran hukumomi sun hallara."

Jihar Legas dai na daga jihohin Kudu maso Yamma da ake yawan samun aukuwar gobara da rugujewar gine-gine a Najeriya.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Bam ya raunata yara 10 a Kaduna, bayanai sun fito

An tafka asara a wata gobarar Rivers

A wani labarin na daban, kayayyakin da suka hada da injinan yankan katako da na’urorin samar da wutar lantarki da kudinsu ya kai miliyoyin naira sun lalace a wata gobara da ta tashi da tsakar dare a jihar Rivers.

Gobarar dai ta tashi ne a babbar kasuwar katako ta Oyigbo da ke laramar hukumar Oyigbo ta jihar Rivers, cewar rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.