Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Sace Matafiya a Titin Ondo-Ekiti

Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Sace Matafiya a Titin Ondo-Ekiti

  • Wasu yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace wasu matafiya a iyakar jihohin Ondo da Ekiti
  • An rahoto cewa maharan sun farmaki fasinjojin ne a tsakanin Ikere-Ekiti da Iju da ke jihar Ondo
  • An gano wasu motoci biyu da babu mutane a cikinsu kuma duk a huje suke da harbin bindiga a wajen faruwar al'amarin

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Akure, jihar Ondo - Rahotanni sun kawo cewa masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wasu matafiya da ba a san adadinsu ba a hanyar Akure/lkere da ke jihar Ondo.

Lamarin ya afku ne a daren ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu, inda aka faka motoci biyu a hanyar. Motocin sune Toyota Corolla da wata farar Highlander duk da bulin harbi a jikinsu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da yan bindiga suka farmaki wata jihar arewa, sun kashe sojoji da mutanen gari

Yan bindiga sun sace matafiya
Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Sace Matafiya a Titin Ondo-Ekiti Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, kakakin yan sandan jihar Ondo, Funmi Odunlami, ta tabbatar da faruwar mummunan al'amarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jarida Punch ta rahoto cewa jami'an sashin yaki da masu garkuwa da mutane na rundunar na aikin kakkabe wasu dazuzzuka a jihohin Ekiti da Ondo.

Jami'ar yan sanda, Odunlami ya fada ma manema labarain batun harin.

"Babu wani rahoto daga yan uwan mamallakan motocin biyu da aka gani a wajen faruwar lamarin a hukumance, kuma babu rahoton batan mutane a jihar."

Sai dai kuma, Odunlami ta bayar da tabbacin cewa rundunar yan sandan jihar za su bankado gaskiyar abun da ya faru ba da jimawa ba tare da ceto mutanen idan har sace su aka yi.

Legit Hausa ta rahoto cewa garkuwa da mutane don kudin fansa ya zama babban matsala a Najeriya yayin da guggun masu laifi ke farmakar manyan tituna, gidaje da ma sace yara daga makarantu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan sanda sun ceto wani mutum da aka sace a Abuja, an kama mai garkuwan

Yan sanda sun cafke matashi a Abuja

A wani labarin kuma, mun kawo cewa Hukumomin yan sanda a babban birnin tarayya Abuja sun yi watsi da rahotannin da ke yawo game da batun garkuwa da mutane da ya afku a rukunin gidaje na River Park a safiyar Asabar, 20 ga watan Janairu.

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, rundunar yan sandan FCT ta bayyana rahotannin a matsayin kanzon kurege sannan ta nanata cewa babu wanda aka sace a rukunin gidajen River Park.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng